Advertisement
Labaran Hausa

Daddy Hikima, Ali Jita, Ali Nuhu sun zama jakadun wani sabon kamfanin sufuri

Daddy Hikima, Ali Jita, Ali Nuhu sun zama jakadun wani sabon kamfanin sufuri

Jaruman Kannywood biyu wato Ali Nuhu da Adamu Abdullahi wanda aka fi sani da Daddy Hikima da kuma mawaki Ali Jita, sun zama jakadun wani sabon kamfanin sufuri mai suna “Legend’s Ryde”.

Mujallar Fim ta fahimci cewa, kamfani ne mai karfi a intanet da yazo daga kasar Indiya tare da hadin gwiwar Hadaddiyar Daular Larabawa “UAE” da kuma Nijeriya.

A ranar Laraba 5 ga watan Oktoba 2022 kamfanin ya kaddamar da ofishin sa na Kano, a yau kuma ya kaddamar da wani ofis din a Jigawa.

Da ma sun fara kaddamar ofis din su na Jihar Osun a ranar Asabar 1 ga watan Oktoba, sai na Abuja a ranar Litinin 3 ga Oktoba.

Ba ‘yan Kannywood kadai suka nada a matsayin jakadun nasu ba har tsohon dan kwallon kafar Nijeriya din nan Kanu Nwanko, da kuma wasu jaruman Nollywood.

Sanya fuskokin sanannun jarumai da mawaka a talla da daddiyar dabara ce ta jan hankalin jama’a, kuma ‘yan Kannywood da dama suna cin moriyar wannan tsarin.

Sai dai mujallar Fim bata gano ko nawa ne aka tsadance aka biya su Ali Nuhu don su tallata wannan kamfanin ba.

Rahoto daga👉 Fim Magazine

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button