Advertisement
Labaran Hausa
Trending

Dalilin Da Yasa Aka Tura Dan Barkwanchi TikTok Mubarak Uniquepikin Gidan Yari

Dalilin Da Yasa Aka Tura Dan Barkwanchi TikTok Mubarak Uniquepikin Gidan Yari

Kotun Majistiri mai lamba 58 da ke Nomansland a Kano ta aike da wasu matasa masu wasan barkwanci zuwa gidan yari.

An gurfanar da matasan yan wasan Barkwancin Mubarak Muhammad da aka fi sani da Uniquepikin da mai ja masa baki Nazifi lsah Muhammad a gaban Kotun bisa zarge-zarge guda hudu.

Hukumar tace fina-finai ta Kano ce ta yi kararsu bisa zargin hada kai, da bata suna da cin zarafin Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje tare da yunkurin tayar da hayaniya a wani faifan bidiyo da suka fitar.

Yayin zaman Kotun na yau Laraba wadanda ake zargin sun amsa tuhumar da ake musu.

Lauyan da ke kare su da iyayensu, sun roki kotu da ta yi musu afuwa.

A nan ne kuma alkalin Kotun mai shari’a Aminu Gabari ya dage shari’ar zuwa ranar Litinin 7 ga watan Nuwamban da muke ciki.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button