Advertisement
Labaran Hausa

Dalilin Da Yasa Matar Daraktan SSS Tasa Aka Tsare Dan Takarar Gwamnan Kano Abba Gida – Gida

Dalilin Da Yasa Matar Daraktan SSS Tasa Aka Tsare Dan Takarar Gwamnan Kano Abba Gida - Gida

Matar Daraktan SSS ta sa an tsare Abba Gida- gida tare da barazanar kashe hadiminsa a filin jirgin sama a Kano

Mai dakin Darakta-Janar na hukumar jami’an tsaro na farin kaya, SSS, Aisha Yusuf Bichi, ta bada umarnin a tsare dfan takarar gwamna na jamiyyar NNPP a Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ta hana shi hawa jirgi da ga Kano zuwa Abuja.

DAILY NIGERIAN ta jiyo cewa dambarwar ta faru ne a kofar shiga hangaren matafiya masu alfarma na filin jirgin saman Malam Aminu Kano, yayin da ayarin motocin Yusuf, wandaa ka fi sani da Abba Gida-gida, su ka haifar da cinkoso.

Lamarin ya haifar wa da ayarin motar Aisha Bichi tsaiko, yayin da ta ke shiga bangaren domin tashi zuwa Abuja.

Majiyoyi sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa lamarin ya fusata Aisha Bichi, inda dogaranta su ka rika duka kan mai uwa da wabi da ababen hawa saboda “taina Hajiya.

Shaidun gani da ido sun ce da kurar ta lafa, sai Abba Gida-gida ya je don ya yi mata korafin abinda dogaranta su ka yi, a matsayin ta na kawar mai dakin sa, inda ta rika yi masa balbalin-bala’i, har ta ke cewa ba za ta bari ya yi gwamna a Kano ba.

Daga nan dai, in ji majiyoyi, sai ga karin jami’an tsaron farin kaya sun zo, inda su ka tsare Abba Gida-gida har sai da Aisha Bichi ta shiga jirgi ta tashi zuwa Abuja.

Wasu majiyoyin ma sun ce kafin ta tashi zuwa Abuja, a lokacin da ta ke ta facfa, Aisha Bichi ta hango wani hadimin Abba Gida-gida, Garba Kilo yana daukar ta a waya, inda ta sa dogaran ta su “harbe shi kuma ba abin da za a yi.”

“Ta ci gaba da fad’a, ta kuma rantse cewa Abba Gida-gida ba zai shiga jirgi daya da ita ba. Haka dai aka ci gaba da tsare Abba har sai da jirgin ya tashi matar Daraktan,” in ji majiyar.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button