
Dalilin Daya Ake Cewa Fim Ne Ke Son Jaruma Zainab Indomie Ba Ita Ke Son Fim Ba
Dalilin Daya Ake Cewa Fim Ne Ke Son Jaruma Zainab Indomie Ba Ita Ke Son Fim Ba
Zainab Jndomie babu ja tana daga cikin jaruman kannywood da daukakar su da shahara ta kai kololuwa har zuwa matakin da kowacce jaruma ke mafarkin kaiwa a yayin da take sharafi a masana’antar kannywood kafin daga bisani wasu tulin kalubale su Janyo Jarumar har ta dauke wuta daga masana’antar gaba daya
Sai dai koda jarumar ta bar fitowa a finafinai ana kewar ta musamman wajen kwarewar ta a acting bin waka furta kalami da sauran abubuwa wanda ke burge yan kallo a wasu lokuta akan wanda wani sa’in ma ana yan TikTok Suna Amfani Da acting na ta na baya ana wallafawa a shafukan sada zumunta
Sai dai tun daga wacan tafiya da zainab tayi sai ya zamana tana yiwa harkar ta film asha ruwan tsuntsaye sai ta dawo gadan gadan kamar zata dora daga inda ta tsaya sai dif asake neman ta a rasa wanda yban gidan ta Adam A Zango ke yi mata kokari wajen dawo da martabar ta da zarar ta watsar da arka ta dawo inda yakan saka ta a finafinai manya ko hada ta da abokan harka ta cigaba da fitowa a manyan finafinai kamar abin zai dore sai ji ta kara watsarwa
Saidai sabanin duk sauran jaruman da ke barin masana’antar bayan dogon lokaci su dawo sun rara gefe ko su rasa masu tafiya da su Zainab duk sanda ta dawo kamar film din jiran ta yake sai kaga ta fito a shaharrun finafinan da suke tashe a lokacin ko kuma ayi mata film finafinan da zasu kara dawo da darajarta kamar dai sanda ta dawo kwatsam aka ganta a shirin Basaja Takun farko da takun karshe da finafinai irin su dakta bahijja da sauran su
Haka zalika a wannan karon ma da ta sake dawowa Adam A zango ya saka ta a shirin sa mai dogon zango dake da dubbunnan makallata Wato Asin da Asin haka zalika an gantà a A wurin daukar shirin Alaqa na li nuhu wanda yake nuna zata samu gurbi a cikin wannah mashahurin shiri shima da wannan muka ce film ke son ta ba ita ke son film ba domin wannan karon ma ba tabbaci Dan Za’a Iya jin ta Kara Komawa Gidan jiya
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.