Advertisement
Labaran Hausa

Dan China Da Ya Kashe Ummita Ya Bayyana Irin Makudan Kudin Da Ya Kashe Mata

Dan China Da Ya Kashe Ummita Ya Bayyana Irin Makudan Kudin Da Ya Kashe Mata

Yanzunan Majiyar Ta Sami Wallafa Daga Shafin Garkuwanarewa Dake Nuni Da Cewar Dan China Da Kashe Ummita Ya Bayyana Irin Makudan Kudin Da Ya Kashe Mata Kamar Yadda Suka Wallafar Cewar

Dan China da ake zargi da kisan Ummita ya ce Naira Miliyan 60 ya kashe mata

A yau Laraba ne dai dan Chinan nan mai suna, Frank Geng Quangrong, wanda ake zargi da kisan masoyiyar sa Ummukulsum Sani, wacce akafi sani da Ummita, ya fara kare kansa a kotu.

Quangrong ya shaida wa kotun cewa shi Musulmi ne kuma ya na aiki a wani kamfanin tufafi a kasuwar Kantin Kwari ta jihar Kano.

Ya bayyana cewa sun hadu da marigayi Ummita ne a 2020, bayan da ta samu lambar wayar sa a wajen wata kawar ta, inda ta nuna tana son shi kuma za ta aure shi.

Jaridar Justice Watch ta rawaito cewa dan Chinan ya ce bayan ya amince da ita, sai su ka fara soyayya, inda ta rika karbar kudade a wajen sa, ya kara da cewa “haka na rika bata duk abinda ta roke ni sabo da bana son na bata mata rai. Ma kashe mata kimanin Naira miliyan 60.

Ya kara da cewa har gida na miliyan 4 ya sai mata, amma sai ji yayi ta yi aure, bar hakan ya bata masa rai ya koma Abuja da zama.

“Amma duk da haka ta rika kira na tana hira da ni ta WhatsApp. Bayan nan ta ce min auren ya mutu, shine
soyayyar ta mu ta dawo,

A cewar sa, wata rana ta tambaye shi kudi shi kuma ya ce bashi da shi, shi ne Ummita ta yi fushi da shi har ta deba kula shi.

“Kawai sai ta ce min ta samu wani saurayin, har ma ta turo min hoton ta da shi sabon saurayin nata, lamarin da ya fusata ni” in ji shi

Alkalin kotun, Sanusi Ado Ma’aji. ya bada umarnin a ci gaba da tsare Quanrong a gidan yari, sannan ya dage zaman zuwa gobe Alhamis domin ci gaba da sauraron kariya.

Ka Wallafawar Tasu

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button