Advertisement
Magunguna

Dan Uwa Ga Abubuwan Dake Haddasa Saurin Inzali Da Ya Kamata Ku Sani

Dan Uwa Ga Abubuwan Dake Haddasa Saurin Inzali Da Ya Kamata Ku Sani

Haryanzu dai babu wani sahihin bayani ko dalili dake bayyana dalilin saurin kawowa ba, saidai wasu bayanai akan dalilan da ka iya bada haske gameda matsalar saurin kawowa ga maza (premature ejaculation). Sune kamar haka:

1. Matsalar rashin karfin mazakuta (erectile dysfunction). Idan namiji baya da karfin gaba to akwai yiwuwar asami saurin kawowa lokacin jima’i , haka kuma, idan akwai karfin zakari to akwai yiwuwar dadewar yin jima’i mai tsawo tsakaninin ma’aurata biyu. Saboda haka, saurin inzali na iya zama wani lokacin alama ce ta rashin karfin zakari.

2. Yanayin halittar wasu mazajen. Wani haka Allah Ya halicce sa ko minti 1 baya iya yi da mace. Amma wannan baya nufin baza’a iya samun saukin yanayin ba. Za’a iya neman magani ko Allah Yasa a dace

3. Samuwar hadari (accident) wanda zai iya shafar al’aurar mutum. Hadari wanda ya shafi lafiyar al’aura na iya haddasa matsalar saurin kawowa.

4. Magungunan kayan mata/da’a da mata keyi. Magunguna na matsi da mata ke sakawa cikin gaba domin matse/tsuke farji. Idan mace tayi amfani da wani magani gabanta ya tsuke/matse fiye da yanda maigidanta ya saba jinta zai iya sa maigidan yayi saurin kawowa saboda karuwar dadi ko dandanon jima’i.

5. Cututtuka masu shafar lafiyar jima’i, kamar cututtukan sanyin mara na maza da mata.

6. Ciwon damuwa ko fargaba na iya haddasa saurin inzali. Misali, idan mutum yayi sabuwar amarya budurwa ko bazawara , idan yana fargabar ko zai iya gamsar da ita ko damuwa akan wani abu, wannan tunani zai iya sanya saurin inzali a cikin saduwar su.

7. Yin istimina’i da gaggawa ( quick masturbation) da wasu matasa keyi kamin suyi aure, musamman yara don gudun kada a kamasu (wasa da al’aura ko zinar hannu). Yana shafar lafiyarsu, yana haddasa saurin kawowa lokacin jima’i.

8. Gado daga wajen mahaifan mutum (inherited traits). Akwai yiwuwar mutum yayi gadon saurin kawowa daga mahaifinsa ko kakansa ko wani jininsa, wato tsatstsonsa. Wato haka duk “family” nasu suke amma bai sani ba.

9. Matsananciyar sha’awar yin jima’i. Idan mutum ya kosa yayi jima’i , fitinar sha’awarsa ko kamuwa da yawa zata iya sanya shi yayi saurin kawowa da zaran zakarinsa ya shiga jikin mace ba tare da bata wani lokaci ba.

10. Rashin wasanni tsakanin ma’aurata kafin saduwa ta yanda macen zata iya fara biyan bukatar ta da wuri kafin maigida ya fara jima’i da ita ta gaba da gaba .

11. Sauyin abokiyar saduwa/ sabuwar amarya budurwa ko zawara. Yanayin sabuwar abokiyar rayuwa, wato sabuwar amarya ga maigida nada tasiri ga kwalwar namiji, yana sanya namiji ya rikice ko ɗimauce da ɗauki wanda hakan zai sanya shi saurin kawowa. Bugu da kari, Binciken ilimi na kiyimiyya ya nuna cewa samun sabuwar abokiyar saduwa (mata) na sanya maniyyin namiji inganci da kyau fiye da nada
.
13. Canza salon kwanciyar aure, musamman mutum kada yayi kwanciya da iyalinsa wacce zata sa zakarinsa ya shige duka cikin gaban ta. Nutso (deep penetration) nasa saurin inzali.

14. Nau’in wasu magungunan. Akwai wasu magungunan da “side effects” nasu zai iya haddasa saurin kawowa ga mutum. Da sauransu, mu takaita haka.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button