
Dan wasan kwallon kafa Sadio Mane yana zuwa tayamu wanke bandakin Masallaci, cewar wani Limami
Dan wasan kwallon kafa Sadio Mane yana zuwa tayamu wanke bandakin Masallaci, cewar wani Limami
Shahararren dan wasan nan na kasar Senegal “Sadio Mane” ya sha yabo sosai bayan an bayyana wani muhimmin aikin alkhairi da yake yi.
Sadio Mane wanda yanzu haka yana taka leda a kungiyar “Bayern Munich” ta kasar Germany bayan ya baro kungiyar Liver pool ta kasar Ingila, ya samu wannan yabon ne daga limamin wani masallaci a birnin Liver pool, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito
Limamin masallacin ya bayyana cewa, duk da daukaka da tarin dukiya da dan wasan yake da ita, hakan bai hana shi zama mai kankan da kai ba.
Dr Muhammad Salah shine ya bayyana abin da limamin masallacin ya fadi game da dan wasan a shafin sa na Facebook.
A cewar limamin Sadio Mane yana da tsadaddiyar mota kirar Bentley amma idan ya tashi zuwa masallaci bada ita yake zuwa ba.
Ga abinda limamin yake cewa akan Sadio Mane: Sadio yana zuwa masallaci a kai a kai, a gidan sa yana da mota kirar Bentley, amma yana zuwa wurin mu cikin karamar mota mara tsada.
Ba ya fitowa neman suna, kuma baya da girman kai, har taimakawa yake
wurin wanke bandakin masallacin.
Wannan dai ba shine karo na farko da wani halin kirki na dan wasan yake bayyana ba, ko a baya an sha kawo labarai kan abubuwan alkhairi da dan wasan yake yiwa al’umma musamman a kasar sa ta Senegal.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa