
Dole mawaki Rarara yana kaiwa wakokinsa Hukumar Tace Fina-finai don a tan-tance su, cewar Gwamnatin Kano
Dole mawaki Rarara yana kaiwa wakokinsa Hukumar Tace Fina-finai don a tan-tance su, cewar Gwamnatin Kano
A dai dai lokacin da dangantaka ke kara tsamari tsakanin fitaccen mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara, da jami’an gwamnatin jihar Kano bisa zargin gwamnan jihar Kano “Dr. Abdullahi Umar Ganduje” da yin uwa da makarbiya wajen cire sunan mawakin daga cikin jerin sunayen ‘yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na tutar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.
Tun da aka tsayar da Mataimakin Gwamna “Nasiru Yusuf Gawuna” ba’a ji Rarara yayi masa waka ba.
An dai jiyo mawakin ya yi wa dan takarar gwamna a jam’iyyar ADC, Sha’aban Sharada waka.
To sai dai ana tsaka da wannan dan barwa ne aka jiyo daya daga cikin hadiman gwamnan kuma mai baiwa gwamnan shawa kan sha’anin Farfaganda wato fitaccen jarumin barkwanci Mustapha Badamasi wanda aka fi sani da Naburaska.
Na jaddada cewa, dolene mawakin ya fara kai wakokinsa Hukumar Tace Fina-finai ta jihar Kano, domin a fara tan-tance wakokin sa.
Labarai24 ta rawaito cewa, ta cikin wani bidiyo da jarumin ya wallafa a kafar sada zumunta ta zamani yace, ina so Rarara ka dakata haka “Abdul Amart” nawa ne shi ma Rarara nawa ne to, sai dai ta wani bangaren ka saki layi.
Don haka duk wakar da kayi ka keta Hukumar tace Fina-finai ta tace, in kaki ka kai to kuwa zaka jawowa shi shugaban tace Fina-finan domin aikin sa ne, a cewar Naburaska.
Duk da dai maganganun jarumin na zuwane ta sigar shagube ga Shugaban Hukumar Tace Fina-finai duba da yadda a baya aka samu rashin jituwa tsakanin jarumin da Hukumar kan yadda hukumar ta shahara wajen kama wasu daga cikin mawakan da basa cikin tsarin tafiyar gwamnatin APC,.
Kafin ayyana ficewarsa daga tsagin tafiyar dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar NNPP “Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso” zuwa gwamnati mai ci ta APC.
To sai dai har zuwa yanzu mawakin bai magantu ba kan wannan batu.
Rahoto daga👉 Hausaloaded