Advertisement
Magunguna

Duk Namijin da yake gajiya ko saurin kawowa yayin da yake saduwa da iyalinsa to ga yadda zaka magance matsalar

Duk Namijin da yake gajiya ko saurin kawowa yayin da yake saduwa da iyalinsa to ga yadda zaka magance matsalar

Hanyoyin magance saurin inzali suna da yawa wasu hanyoyin na yiwa wasu aiki, wasu kuma sabanin haka don haka ga hanyoyi da mutum zai jarraba domin neman dacewa akan wannan matsalar

Mai saurin inzali yakamata ya cire tunanin jima’i daga kwalwarsa a lokacin da yake saduwa da iyalinsa, domin kuwa hakn shi ne zai hana shi saurin kawowa.

Matsanancin tunani ko kamuwa da yawa kafin fara jima’i zai iya sanya mutum ya kone tunkafin ya tafasa.

Masana sun nuna cewa, bujiro tunanin wani abu a cikin rai wanda ba jima’i ba marar dadi a lokacin saduwa na karawa mutum tsawon lokaci ba tare da ya lura da hakan ba.

Daukan jima’i baya baya, abinda zai taimakawa mai matsalar saurin kawowa shine rage yawan tunanin jima’i yake aikatawa, ko kuma ya baryin tunanin cewa yana yin jima’i ne domin samin gamsuwa wacce iyalinsa da yake sha’awa take biya masa.

Kamata yayi tunaninsa ya kasance cewa yana aikata jima’i ne domin ya biyawa iyalinsa bukatar farko kamin tasa.

Abubuwan da za’a nema domin magance wannan matsalar ta saurin inzali sune kamar haka:

A nemi kubewa danya guda 5 a wanke sa’annan a yanke gutsun-gutsun a cikin tukunya, sai a sami kofi daya na ruwa a zuba cikin tukunyar sa’an nan a daura akan wuta a rufe tukunya.

Da zaran ruwan ya tafasa sai a sauke tukunya a tace ruwan a kofin shayi, sai a zuba Zuma domin ta bada dandano a bari ya huce kadan amma asha da dumi.

Ayi haka sau 2 a rana har na tsawon kwana 10 ko fiye da haka, kubewa nada sinadari mai amfani mai sanya jinkirin kawowa a lokacin da Namiji yake saduwa da iyalinsa.

A nemi citta musamman danya a wanke a kuma kankare ta sannan a dake ta ayi shayi da ita, bayan an tace ta a kofin shayi sai a zuba zuma ta bada dandano sai a sha shayin da dumi, ayi hakan safe da rana.

Ita ma Citta nada sinadari mai zafi na “gingerol” mai sanya yawan gudanar jini ga al’aura, wanda hakan na sanya karfin gaba da jinkirin kawowa a lokacin jima’i.

A nemi man na’a-na’a mai kyau dan Misra ko na kamfanin Hemani, a wanke gaba da ruwan dumi a goge lemar sannan a shafa man ga Azzakarin ya shiga fata, da tsawon sandar zakari amma banda kofar fitsari.

Musamman a shafa idan Azzakari yana mike, sai a jira bayan minti 10 zuwa 15 sannan a sadu da iyali.

Man na’a-na’a na rage “sensitivity” na zakari, wato rage kaifin dandano da zakari keji ta yanda zai hana saurin kawowa a lokacin saduwa da iyali.

Haka kuma za’a iya amfani da man kanimfari mai kyau a maimakon man na’a-na’a, bugu da kari man kanimfari na maganin karfin gaba.

Fita daga gaban mace na yan mintoci a lokacin da mutum yaji ya kusa kawowa, da kuma fita daga cikin farji da matse kan zakari da hannu a lokacin da mutum yake akan hanyar kawowa, shima yana sanya Namiji rashin saurin kawowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button