Advertisement
Labaran Hausa

Furodusar kannywood Fatima Ibrashim Lmaj ta taya Yusuf Custome tare da amaryarsa Maryam murnar auren su

Furodusar kannywood Fatima Ibrashim Lmaj ta taya Yusuf Custome tare da amaryarsa Maryam murnar auren su

Furodusan Masana’antar Kannywood, Hajiya Fatima Ibrahim Ahmad (Lamaj), ta yiwa Yusuf Nagazara wanda aka fi sani da Yusuf Costume da amaryar sa Maryam fatan zaman lafiya mai dorewa, kamar yadda “Fim Magazine” suka ruwaito.

Lamaj, wadda ita ce tsohuwar shugabar kungiyar MOPPAN reshen jihar Kaduna, tayi wannan addu’ar ne bayan an daura auren Yusuf, wanda yaron kamfanin ta ne.

Da take bayyana wa mujallar Fim irin farin cikin da tayi na ganin auren Yusuf, babbar furodusar tace, A matsayi na na uwa ga ango da amaryarsa Maryam ina yi masu fatan alkhairi da zaman lafiya mai dorewa.

Lamaj ta cigaba da cewa, Yusuf yaron kamfani na ne a nan ya fara aikin costume, yana da hankali da sanin ya kamata.

A yanzu yana kasuwanci a Abuja amma duk da haka bai bar harkar industiri ba, domin har yanzu in zan yi aiki yana aiko min da costume, gaskiya Yusuf bai manta da mafaba.

Ina fatan Allah yayi masu albarka, ya basu zaman lafiya da zuri’a dayyiba, nayi matukar farin ciki da wannan aure.

An daura auren Yusuf da Maryam ne a ranar Asabar 8 ga watan Oktoba 2022, da misalin karfe 2:00 na rana a garin Makarfi dake jihar Kaduna, a kan sadaki N200,000.

An yi dina a daren ranar daurin auren a otal din “Silver Sand” dake Titin Katuru Unguwar Sarki Kaduna.

Kafin ranar daurin auren, an yi bikin Kamu a Orage Hotel dake Hayin Banki, Kaduna.

Allah ya basu zaman lafiya da zuri’a dayyiba ameen.

Rahoto daga👉 Fim Magazine

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button