Advertisement
Magunguna

Ga masu yin wasa da azzakari ga hanyoyin da zakubi domin kaucewa aikata istimna’i wato wasa da al’aura

Ga masu yin wasa da azzakari ga hanyoyin da zakubi domin kaucewa aikata istimna’i wato wasa da al’aura

HANYOYIN KAUCEWA AIKATA ISTIM’NA’I CIKIN SAUKI.

1. Kaucewa kallon finafinai batsa.

2. Dena kallon photon da tsiraici yayi yawa a ciki.

3. Dena zama kai kadai.

4. Rage mu’amala da mace wacce ba muharramar ka ba.

5. Rage zancen batsa yayin waya ba wata ko wani.

6. Rage yawan tunanin mace ko namiji.

HANYOYIN DA ZAA BI DON DENA AIKATA ISTIM’NA’I.

1. Tuba ga Allah tare da daukar Alkawarin rashin sakewa har abada.

2. Bijirewa dukkan wani nau’in abu mai tayar maka da shaawa.

3. Rage yawan jakkon finafinai a waya ko a TV.

4. Koda kaji idan baka yi shiba kamar zaka mutu ka daure karka aikata shi.

5. Rage zama a waje kaikadai don hakan zai taimaka maka, karka tuna abunda zai saka jmka aikata shi.

A takaice wadan nan suna wasu habyoyi da insha Allah mai aikata wannan zai bi domin dena aikata shi.

Maganin kwanciyar azzakari a lokacin saduwa.

Yan uwa maza da yawa suna fama da matsalar rashin mikewar Azzakari ya tsaya yayi karfi wanda ake kira (Erectile dysfunction) wacce ake kira (ED) wannan cuta ta zama ruwan dare a rayuwar mazaje.

Kuma wannan matsala tana da wuyar shaani kasancewar ba lalura daya ke haifar da ita ba,cutuka da yawa sukan jawo wannan lalaura.

Hakan yana faruwa Sanadiyyar rashin shigar isashshen jini cikin jijiyoyin Azzkari wadan da sune ke saka shi mikewa ya tsaya yayi kwari da kuma karfi.

MENENE KE JAWO WANNAN CUTA.

Kamar yadda muka fada a baya cutuka da yawa suna iya jawo wannan lalaura amma ga kadan daga cikin su.

1. Ciwon zuciya:Lallai wadan da suke fama da lalurar zuciya suna fama da wannan matsalar ta Ed sakamakon zuciya ita ce harba jini zuwa kowannne sassa na jikin dan Adam, da zarar ta samu rauni to hakan zai saka baza ta iya harba jini yadda ya kamata a kowanne sassa ba,hakan zai jawo jini bazai shiga mazakuta yadda ake so ba.

2. Prostate cancer (cutar kansa ta futustota) wannan wata cuta ce da take tsirowa a cikin prostate na maza,hakan yana jawo matsalar rashin mikewar Azzakari a lokacin shaawa.

Sannan wanda aka yiwa aikin wannan Cancer shima matsakar tana samun sa,saboda yanke jijiyo da ake a lokacin aikin.

3. Prostate enlargement wannan itama cuta ce wacce take haifar da kumburi a futustota ta da Namiji wanda hakan yake tushe hatta hanyar da fitsari ke fita, sakamakon hakan Azzakari bazai rika mikewa yadda ake so ba.

Sannan shan magunguna na wannan matsala suna jawo rauni ga Azzakari.

1. Yawan kiba.

2. Ciwon suga.

3. Yawan kitse.

4. Ciwon koda.

5. Karancin hormones (testosterone).

MATSALOLIN DA SUKE JAWO WANNAN CUTA WADAN DA BA LALURA BA.

1. yawan damuwa.

2. Yawan tunani.

3. Bacin rai.

4. Matsala a tsakanin ma’aurata.

A takaice wadan nan sune masu matsaloli dake jawo matsalar raunin Azzakari da ake kira da (Erectile dysfunction).

Allah yasa mudace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button