Advertisement
Magunguna

Ga yadda zaku gyara nonuwanku suyi kyau koda sun zube kamar na tsofi

Ga yadda zaku gyara nonuwanku suyi kyau koda sun zube kamar na tsofi

Yaku yan uwana mata shi kwantaccen nono kansamuwa ta hanya iri daban daban wasu nonuwansu kan kwanta sakamakon shayarwa da suke wasu kuma nasu kan kwantawa ne saboda wani yanayi musanman yan matan dabasuyi aure ba.

To insha Allahu daga yanzu wannan magani zai dago miki da kwantaccen Nonanki yar uwa kedai ki nutsu kuma kiyi yadda akace.

Abubuwan da zaku nema domin hada wannan maganin sune kamar haka.

(1) Farar shinkafa ta tuwo.

(2) Jar Masara.

(3) Alkama.

(4) Gero.

(5) Nono ko Yogot.

Idan kun samo wadannan abubuwan da muka lissafa muku ga yadda zakuyi hadin nasu.

Kisamu wadannan Farar shinkafa, Jar Masara, Alkam, Gero din nan naki saiki wanke su ki shanyasu su bushe saiki dan soyasu sama-sama sai a nika miki su, amma kuma zaki iya dakawa idan kina da karfin haka.

Saiki tankade bayan an nikasu kenan ko an daka, bayan kin tankade din saiki samu nono mai kyau ko kuma Yagot ta asali saiki debi wannan garin naki da kika tankade cokali daya da rabi ko biyu saiki dinga zubawa a wannan Nono naki ko yagot saiki juya sosai saiki shanye.

To yar uwa insha Allahu indai matsalar kwanciyar Nonuwanki ne to ta kawo karshe, yar uwa nonuwanki zasu dawo kamar na sabuwar budurwa, kuma zasuyi laushi da yaddar Allah.

Allah ya bada ikonyi kuma a turawa ‘yan uwa Mata don suma su amfana.

Amma abin lura a nan shine, Amma Idan kinsan zakiyi yaye Kada kiyi, ki bari sai kinyi yayen kin gama warkewa daga cutar da ake fama da ita ta yaye , saikiyi kayanki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button