Advertisement
Labaran Hausa

Gadon waka nayi domin mahaifina Makadi ne, cewar Yawale Dan Kurma na Kwana Casa’in

Gadon waka nayi domin mahaifina Makadi ne, cewar Yawale Dan Kurma na Kwana Casa'in

Jarumin Kannywood “Auwal Ishaq” wanda aka fi saninsa da Yawale Dan kurma a cikin shirin fim din Kwana Casa’in mai dogon zango ya bayyana cewa, yafi daukar kansa a matsayin mawaki duk da anfi sanin sa a jarumi.

A tattaunawar da Mujallar Fim tayi da Auwal ya bayyana cewa, a sali shi mawaki ne, sai dai yafi shahara a fim kasancewar ya fara fitowa a fina-finan Adam A Zango ne, daga bisani kuma ya fara fitowa a Kwana Casa’in.

Yace, akan sanya shi a bangaren barkwanci ne kafin ya fito a matsayin Yawale Dan kurma a Kwana Casa’in.

A cewarsa: Amma gaskiya duk da nayi suna a shirin Kwana Casa’in nafi daukar kaina a matsayin mawaki a halin yanzu, sabida duk abinda na sanya a raina zan yi sai Allah ya taimake ni nayi nasara.

Hakan yasa ko dana fara fim banji a jikina cewa ba zan iya ba, ita kuma harkar waka zan iya cewa na gada ne kasancewar mahaifina makadi ne, don haka a wurinsa nagada.

Yayin da aka tambaye shi dangane da daukakar da ya samu cewa yayi: A harkar fim nafi daukaka musamman a shirin Kwana Casa’un, duk inda naje sai inji ana kirana da Yawale Dan kurma ko kuma saurayin Rayya.

Sanadin fim naje kasashe kamar Ghana, Nijar, Chadi, Kamaru da sauran manyan garuruwa a cikin kasarnan, kuma muna fatan wannan daukakar da muka samu ta kai mu ga gamawa lafiya.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button