Advertisement
Labaran Hausa

Gaskiyar magana akan rashin lafiyar jarumi Balarabe Jaji

Gaskiyar magana akan rashin lafiyar jarumi Balarabe Jaji

Jarumin Kannywood “Alhaji Balarabe Jaji” ya yi bayani kan wasu hotuna da aka yada a Facebook inda aka nuno kwance magashiyan a asibiti, da alamar ba ya da lafiya.

A cikin ‘yan kwanakin nan ne hotunan suka bulla inda aka ga Alhaji Balarabe Jaji yana kwance a asibiti, idon sa daya da bandeji.

Wasu da suka ga hotunan sun yi tunanin a fim ne, yayin da wasu kuma ke tunanin da gaske shine aka yi wa aiki a ido.

Mujallar Fim ta amsa kiran mutane da dama masu tambayar gaskiyar lamari a kan hotunan, kamar yadda “Fim Magazine” suka ruwaito.

Wakilin mu ya tuntubi shahararren jarumin kuma ya tabbatar masa da cewa lallai aiki aka yi masa a idon sa daya.

Da yake tattaunawa da mujallar Fim jarumin yace, gaskiya ne ido daya ba lafiya an yi mani operation amma na samu sauki.

Ranar Laraba 16 ga Nuwamba 2022 aka yi operation din, a Haske Specialist Hospital Kaduna da misalin karfe 2:00 na rana.

Ko me Balarabe Jaji zai ce wa masoyan sa game da damuwa da suka yi don jin halin da yake ciki? Sai ya ce: Allah ya saka wa kowa da alkhairi an yi aiki kuma aiki ya yi kyau har an bude idon na ga cigaba sosai.

Sabida haka addu’a ya yi matukar tasiri, Allah ya saka masu da alkhairi. Aiki biyu aka yi a idon guda daya, kuma an samu nasarar aikin an yi shi successfully, sabida ‘yan uwa sun taya ni addu’a kwarai.

Don haka a yi min godiya wurin kowa da kowa. Allah ya ba kowa lafiya, wadanda suka rasu kuma a cikin mu, Allah ya gafarta masu ya kuma yafe kurakuran su,

Mu kuma in tamu tazo ya hada mu da su a Jannatul Firdausi. lyalan da za mu bari a baya, Allah ka kula da su da kuma tarbiyyar su. Na gode kwarai dagaske.

Rahoto daga👉 Fim Magazine

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button