
Gaskiyar magana ta bayyana kan yarinyar da ake cewa jaruma Momee Gombe ce ta haife ta
Gaskiyar magana ta bayyana kan yarinyar da ake cewa jaruma Momee Gombe ce ta haife ta
Daga karshe dai gaskiya ta bayyana a kan yarinyar da ake ta yawo da ita ana cewa, jaruma masana’antar kannywood Momme Gombe ce ta haifeta.
Matashin da kwanaki ya fito yayi bidiyo da wata karamar yarinya ‘yar kimanin shekaru 12, inda ya bayyana cewa yarinyar diyace ga jaruma Momme Gombe.
Inda ya fito yayi sabon bidiyo ya bayyana cewa, ba gaskiya bane maganar da yayi a baya na cewa Momme Gombe ta taba haihuwa, hasali ma Momme Gombe auren ta daya kuma kwata-kwata lokacin da tayi aure baima kai har ta iya haifan wannan yarinyar ba.
Yarinyar mai suna Amira kawai yayi amfani da ita ne domin yin raha sabida ita yarinyar ma da ake magana akai kwata-kwata batasan Momme Gombe Ba.
Sannan kuma bata taba ganinta ba sai dai kuma yace, kama da yarinyar take yi da Momme Gombe ne yasa ya fito yayi haka.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken bayani daga bakin mataahin.
Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.