Advertisement
Labaran Hausa

Gwamnan Tambuwal Ya Baiwa Alaramma Mal. Nura Adullahi Kujerar Hajj (4) Tare Da Makudan Kudi

Gwamnan Tambuwal Ya Baiwa Alaramma Mal. Nura Adullahi Kujerar Hajj (4) Tare Da Makudan Kudi

Yanzu nan majiyarmu ta samu wani labari mai dadi wanda anka baiwa Alaramma wanda yazo na farko a gasar Alkur’ani mai girma na inda wannan alaramma dan jihar Sokoto ne shine yau anka bashi wannan kyauta hade da nadashi wata babba saurata.

Kamar yadda shafin gidan gwamnatin jihar Sakkwato na ruwaito a shinsu na sada zumunta facebook inda sunka wallafa kamar haka

“Breaking News!!! Gwamna Tambuwal ya baiwa Hazikin yaron Mal. Nura Abdullahi(Modibbon Sokoto)wanda yayi Nasara a Gasar Karatun Qur’ani ta kasa kyaututtuka kamar haka:

1. Kurerar Hajji (4) Guda tashi da Mahaifiyar sa,da Mahaifin sa da Matarsa.
2. Naira Miliyan 10
3. Daukar Nauyin karatun sa har Phd.
4. Bashi aikin Gwamnati idan ya kare degree.

Allahu Akbar. Irin diyan da kowa ke murnar haihuwa kenan.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bashi Sarautar Modibbon Sokoto.

Allah saka ma Maigirma Gwamna da Alheri.

22 Jan 2023″

Bugu da karin kari majalisar sarkin Musulmi

Gwamna Tambuwal ya mika ma Gwarzon Shekara 2022 na Musabuka da Kudi Naira Dubu 500 daga Fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi.

wanda a cikin hoton nan na kasa yake mika masa kudinda Majalisar sarkin Musulmi ba baiwa alaramma daga nan kuma anka nada shi sarauta.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button