Advertisement
Magunguna

Hanyar Da Zaku Bi Domin Gane Cewar Mace Tana Da Budadden Gaba (Losing Virginity)

Hanyar Da Zaku Bi Domin Gane Cewar Mace Tana Da Budadden Gaba (Losing Virginity)

1. Mafi yawan mata masu fama da matsalar budadden gaba na fama da matsalar rashin rike fitsari, wato digar fitsari. Digar fitsarin zata iya faruwa a lokacinda kika dauki wani abu mai nauyi, ko lokacinda kika yi dariya, tari, ko atishawa. Wannan alamace cewa mace nada budadden gaba.Yawan shekaru. yawan haihuwa. yawan jima’i, tiyatar likita (karin kofa) ko wani rauni a gaban mace, ko tsayawar al’ada (menopause) saboda karancin sinadarin “estrogen” na iya sanya raunin tsokokin farji wanda daga karshe zai iya haddasa budewar tsokokin bangon farji masu matse zakari.

2. Hanya ta biyu da zaki iya sanin ko kina da gaba mai fadi itace: ki saka dan yatsanki guda (manuni) cikin gabanki sa’annan kiyi kokarin matse dan yatsan da tsokokin farjinki. Idan har ki gwada yin hakan kuma ya zamanto baki iya jin kina matse dan yatsan da farji to zaya iya zama kina da babban wuri. Bugu da kari, idan kika saka yatsa 2 ko 3, misali manuninki da kuma yatsan tsakiyar hannnunki (mafi tsawo). kuma baki ji wata alamar bangon farjinki yana matse yatsun ba to yiwuwar itace kina da buddden farji.

3. Idan ya zamanto yana da wuya kamin kiji kololuwar dadi (orgasm)/kawowa lokacin saduwa. Yana iya yiwuwa alamar budadden gaba ne. Haka kuma, raguwar jin dadi ba kamar daba shima na iya zama alamar.

4. Idan ya zamanto mace tana wasa da gabanta domin biyan bukatarta kuma tafi sha’ awar ta saka wani babban abu a gabanta akan karami wato bata jin dadin karamin abu idan ta saka a farji sai babba. shima alamace cewa mace nada girman farji. A baya munyi bayani da tsoratarwa akan wasa da gaba. Yana da illa ga laiya da rayuwar auren ‘ya mace. Don haka sai kiyaye.

5. ldan ya zamanto kina shan wahala kamin ki gamsar da mai gidanki wajen jima’i ba kamar daba.

6. Idan ya zamanto sai kin matse ko hađe Cinyoyin ki biyu sosai sa’annan kike jin dadi jima’i da maigidanki. Wannan ma yana iya zama alamar budadden gaba. Duk da dai cewa wani lokacin yana iya zamantowa mijin ne keda karamar al’aura. Amma idan kamin haihuwarki babu wannan matsalar sai daga baya to sai ki Zargi budewar gaba.

7. ldan ya zamanto kina jin karar fitar iska daga farjinki lokacin da maigidanki yake saduwa dake, iskan kamar fitar “tusa” amma ba tusa bace (fanny farting) kuma babu wari. Iskan yana shiga yana fitowa lokacinda maigida yake kaikawo. Wannan alamace kina da budadden farji.

Allah Yasa Mu Dace

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan Bayanin Zamu So Karben Ra’ayoyinku A Sahen Comment.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button