
Hanyoyin da zaka rabu da aikata istimna’i da kuma yadda za kayi maganin matsalar daya haifar ma
Hanyoyin da zaka rabu da aikata istimna'i da kuma yadda za kayi maganin matsalar daya haifar ma
Mutane da dama sun Dauki istimna’i wato wasa da al’aurar su a matsayin hanyar gamsar da Kan su ba tare da sanin illolin da yake haifar wa a jikin su ba, musamman bayan sun yi aure domin Yana jawo tarin matsaloli bayan wanda yake aikata shi yayi aure ko mace ne ko namiji.
Duk da tarin illolin shi bai hana wasua ikatawa sabida dan jin dadin dake tattare da shi, abin da ya kamata ku sani shine bayan haramtawa da Allah yayi toh a likitance ma yana da illoli masu tarin yawa.
Duk dai a cikin wannan rubutu zaku ga illolin shi, sannan kuma da hanyoyin da zaku bi har ka daina da taimakon Allah, hukuncin sa tare da ma’anar shi.
Menene Istimna’i: Istimna’i shine Mutum ya biyawa Kan shi bukata da kan wajan yun wasa da al’aurar shi har ya kawo ruwa, mace ko namiji wannan shine ma’anar Istimna’i a saukakakken Harshe kuma na san mai karatu ya fahimta ko da bai sani ba a da.
Menene Hukuncin shi a addinin musulunci: Hukunci a addinin musulunci haramun ne bisa ga ljtima’in malamai, wasu ‘yan kadan daga cikin su sun karhanta shi.
Menene illolin Istimna’i: Istimna’i yana da illoli masu yawan gaske shi yasa ake yawan tsawatarwa a kai domin gujewa haduwa da illolin na shi.
Daga cikin illolin da istimna’i yake haifarwa yanzu zamu kawo muku kadan daga ciki.
(1) – Yana sa yawan ciwon Kai.
(2) – Yana jawo ciwon sanyi mai tsanani sosai.
(3) – Yana sa yawan mantuwa da rashin rike karatu.
(4) – Yana haifar da ciwon gabobi da kafadu mai tsanani.
(5) – Yana jawo ciwon daji wato cancer kenan a turance.
(6) – Mai aikata istimna’i yana kasancewa da yawan mantuwa.
(7) – Yana jawo cututtukan mafitsara ga mai yin shi namiji ko mace.
(8) – Idan Mutum yana aikata istimna’i bazai iya biyawa abokiyar zaman shi bukata ba.
(9) – Yana Sanya zuciya ta rika bugawa da karfi.
(10) – Yana sa mutum yawan damuwa kullum zai kasance cikin rashin natsuwa.
(11) – Yana jawo gaban namiji ya zama kankani.
(12) – Yana sa gaban mace ya bushe.
Wadannan sune kadan daga cikin
illolin da aikata istimna’i yake haifarwa, illolin suna da yawan gaske kai dai idan kana cikin masu aikata wa kayi kokarin
dainawa sabida kar lokaci ya kure maka.
Ta wace hanya zaka rabu da aikata istimna’i: Wannan tambayar tana da matukar muhimmaci domin mutane da dama suna yinta.
Idan kana cikin masu tambayar tabbas kasamu maganin matsalar idan Allah Yaso, hanya ta farko itace mutum yaji tsoron Allah ya bari tun kafin fushin Allah ya riske shi.
Idan kana son daina aikata istimna’i, ga wasu hanyoyin da zaka bi.
(1) – Ka daina kallon fina-finan Batsa.
(2) – Ka bar kebewa Kai kadai.
(3) – Ka nisanci duk abinda zai iya tayar maka da sha’awar ka.
(4) – Kayi aure idan kana da halin yin sa, idan baka da Halin yin aure ka yawaita yin azumi.
Wadannan sune hanyoyin da za kabi ka rabu da aikata istimna’i insha Allah.