Advertisement
Magunguna

Hanyoyin da zakubi domin magance matsalar saurin inzali a lokacin saduwa da iyali

Hanyoyin da zakubi domin magance matsalar saurin inzali a lokacin saduwa da iyali

Hanyoyin magance saurin kawowa inzali suna da yawa wasu hanyoyin na yiwa wasu aiki wasu kuma sabanin haka, don haka ga hanyoyi kamar haka da mutum zai iya jarrabawa domin neman dacewa.

A) Bayan kawowar farko, kawowa ta biyu na zuwa da lokaci mai tsawo kafin mutum ya sake fitar da wani maniyyin a karo na biyu.

Don haka idan mutum yana son ya daɗe bai yi inzali ba to ya tari jima’i a karo na biyu wanda zai bashi lokaci mai tsawo kafin yayi inzali.

B) Hanyoyin neman magani na musamman daga Likitan asibiti ko Malamin Islamic Chemist, idan hanyoyin da muka zayyana basu yiwa mutum ba to sai yabi hanyar ganin ɗaya daga cikin wadannan mutanen domin neman taimako.

Akwai wasu hanyoyi da dama na magance matsalar saurin inzali.

C) A nemi man na’a-na’a mai kyau a wanke gaba da ruwan dumi a goge lemar sa’an nan a shafa man ga zakari ya shiga fata ga kai da tsawon sandar zakari, amma banda kofar fitsari musamman a shafa idan zakari yana mike sai jira bayan minti 15 zuwa 20 sa’an nan a sadu da iyali.

Man na’a-na’a na rage kaifin danɗano da zakari keji ta yanda zai hana saurin kawowa lokacin jima’i, haka kuma za’a iya amfani da man kanimfari mai kyau a maimakon man na’a-na’a, bugu da kari man kanimfari na maganin karfin gaba.

D) Fita daga gaban mace na ‘yan mintoci a lokacin da mutum yaji ya kusa kawowa, da kuma fita daga cikin farji da matse kan zakari da hannu a lokacinda mutum yake akan hanyar kawowa.

E) Rage kosawa-kagara-zumudi: Mai saurin inzali ya kamata ya cire tunanin jima’i daga ƙwalwarsa a lokacinda yake saduwa da iyalinsa.

Matsanancin tunani ko kamuwa da yawa kafin fara jima’i zai iya sanya mutum ‘yan ƙone tun kafin ya tafasa, masana sun nuna cewa bujiro tunanin wani abu a cikin rai wanda ba jima’i ba marar daɗi a lokacin saduwa na ƙarawa mutum tsawon lokaci ba tare da ya lura da hakan ba.

Dokin jima’i baya biya, abinda zai taimakawa mai matsalar saurin kawowa shine, rage yawan tunanin jima’i ne yake aikatawa, ko kuma ya bar yin tunanin cewa yana yin jima’i ne domin samun gamsuwa wacce iyalinsa da yake sha’awa take biya masa.

Kamata yayi tunaninsa ya kasance cewa yana aikata jima’i ne domin ya biyawa iyalinsa bukata farko kamin tasa, abin lura, ka ɗauka ma cewa ba jima’i bane kake yi a lokacin da kake saduwa ko tarawa da iyalinka.

F) A nemi kuɓewa ɗanya guda 5 a wanke sa’annan a yanke gutsun-gutsun a cikin tukunya, sai a sami kofi ɗaya na ruwa a zuba cikin tukunyar sa’annan a ɗaura akan wuta a rufe tukunya.

Da zaran ruwan ya tafasa sai a sauke tukunya a tashe ruwan a kofin shayi, sai a zuba zuma ta bada ɗanɗano a bari ya huce kaɗan amma asha da ɗumi.

Ayi haka sau 2 a rana har na tsawon kwana 10 ko fiye da haka, kubewa nada sinadari mai amfani mai sanya jinkirin kawowa ga maza.

G) A nemi citta musamman danya, a wanke a kuma karkare ta, sa’annan a dake ta ayi shayi da ita bayan an tashe ta a kofin shayi sai a zuba zuma ta bada ɗanɗano asha shayin da dumi.

Ayi hakan safe da rana: Citta nada sinadari mai zafi na mai sanya yawan gudanar jini ga laura, wanda hakan na sanya karfin gaba da jinkirin kawowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button