Advertisement
Labaran Hausa

Idan ka sani matarka da ciki sakin dai bai saku ba, cewar Sheikh Nazifi Alkarmawi

Idan ka sani matarka da ciki sakin dai bai saku ba, cewar Sheikh Nazifi Alkarmawi

Wata Fatawa da Sheikh Nazif Alkarmawi yayi kan cewa, idan mutum ya saki mace da ciki ajikin ta bata saku ba ya hadda sa cece-kuce a shafukan sada zumunta.

Musamman kasancewar babban malamin Ahlussunna Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo yayi masa Raddi zazzafa kan wannan fatawa.

Har ila yau wani abu da ya kara daukar hankali kan wannan batu shine yana yin yadda Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo yayi masa Raddin, tare da kausasa harshe inda aka dinga wallafa a shafukan sada zumunta.

Sheikh Nazifi Alkarmawa dai babban Malamin Darikar Tijjaniyya ne, kuma kowa yasan Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo kuwa babban Malamin Izala ne.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikakkun jawaban Malaman.

Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button