Advertisement
Magunguna

illolin da istimna’i yake haifarwa ga namiji ko macen da suke aikata shi

illolin da istimna’i yake haifarwa ga namiji ko macen da suke aikata shi

ZUWA GA MASU AIKATA ISTIM’NA’I WATO WASA DA AL’AURA.

Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu, yan uwa na barkan mu da wannan lokaci inai wa kowa da kowa fatan Alkhairi, da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.

Yan uwa nayi nazarin yin wannan rubutu nawa ne akan, ‘yan uwa masu aikata istimna’i maza ko mata, kamar yadda nayi bayani a baya game da illolin da yake haifarwa da kuma cutarwar sa.

Yan uwa wllahi tallahi istimna’i bashi da wani amfani, duk wanda yace maka ka rika yi yana kara lafiya makiyin ka ne shi, kuma wallahi karshe sai ya saka ka kayi nadama, don na ji kuma an gayan.

Domin aikata wannan abu bayan ka sabawa Allah to kai kanka yinsa yana cutar dakai, kuma yinsa bashi da wata fa’ida ta zahiri ko badini, kuma ga masu cewa suna yinsa ne don gudun afkawa zina, ku sani baka da wata hujja,don ai ba zabi aka baka ba, cewa ka aikata shi idan kana jin tsoron zina!!.

Kamar yadda na fadi illolin sa a baya, yanzu ma gaka zan sake maimaita su, tare da karin wadan su.

KADAN DAGA ILLOLIN SA GA MAZA.

1. Kankancewar azzakari.

2. Saurin kawowa.

3. Fitar fafin ruwa daga gaba.

4. Raunin jiki.

5. Yawan kokonto.

6. Rashin nutsuwa.

7. Saurin tsufa.

8. Yamushewar fatar jiki.

9. Fitsarin jini.

10. Jin zafi yayin fitsari.

11. Rashin samun rabo.

12. Kashe kwayoyin halitta.

ILLOLIN SA GA MATA.

1.Lalacewar farji.

2. Bushewar farji.

3. Faitar farin ruwa daga farji.

4. Daukewar sha’awa.

5. Faitar kuraje daga farji.

6. Gusar da budurcin ya mace.

7. Yamushewar fatar jiki.

8. Saurin kawowa yayin saduwa.

9. Yawan kokonto da rashin nutsuwa.

10.Zobewar Nono.

11. Hana samun rabo.

12. Rasa kwayoyin halitta.

Sannan kuma dukkan wanda ya tsinci kansa cikin aikata wannan babban kuskure,yayi kokarin denawa tun kafin lokacin danasani ya riske shi.

Kuma yayi kokarin yin amfani da maganin daya dace,don kaucewa barazanar, illolinsa kuma shi yana da wani abu koda ace kafi shekara 20 da daina shi muddin baka nemi magani ba to yana nan tare da kai baza ka gane ba sai kana da iyali, ko kayi aure sannan zakaga illar da yayi maka.

Allah yasa mudace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button