Labaran Hausa

Ina farincikin cika shekaru 14 da Matata ba tare da kowa yaji kanmu ba, cewar izzar so Lawan Ahmad

Ina farincikin cika shekaru 14 da Matata ba tare da kowa yaji kanmu ba, cewar izzar so Lawan Ahmad

Fitaccen jarumi kuma furodusa a masana antar Kannywood “Lawan Ahmad” ya bayyana cewa, a zamansu da matarsa “Saratu Abdulsalam” babu wanda ya taba kai karar wani a tsakanin su tsawon shekaru 14 da aure.

Mujallar Fim ta zanta da jarumin inda yace, yana matukar farin ciki tare da alfahari da cika shekaru 14 a ranar 25 ga watan Oktoban 2022, ba tare da an ji kansa da matarsa ba.

Ya wallafar zazzafan hotonsa tare da uwar ya’yansa don murnar, yayin tattaunawa da Mujallar Fim, jarumin ya ce:

Alhamdulillah, ina farin ciki tare da alfahari da Allah cikin ikon sa yasa muka cika shekaru 14 da aure.

Kuma babu wani a cikin mu da ya taba kai karar wani gidan iyayensa, muna zaune da dadi babu dadi har muka cika shekarun nan.

Tabbas ba karamin abin alfahari bane wannan kuma ba karamar ni’ima bace da Allah yayi mana tsawon shekarun nan, gaskiya ina matukar farinciki.

Lawan yana daya daga cikin ‘yan fim wadanda babu wanda ya taba jin wani mummunan labari tsakanin sa da matarsa, duk da yadda jama’a ke kallon ‘yan fim ba sa rike aure.

Yayin da aka tambaye shi ko zai yi karin bayani, ya bayyana cewa:

Babu wanda ba ya zaman aure, dama idan har aka yi aure akwai saki kuma addini ma ya amince da hakan kowa ya riga ya sani.

Kuma dalilin da yasa ake ganin kamar ‘yan fim basa zaman aure sabida komai nasu a bude yake.

Ya bayyana cewa, da zarar dan fim ya bayyana wani abu ko ya wallafa shi, nan da nan mutane zasu dauka su cigaba da yadawa, hakan ya biyo bayan yadda kowa ya san su.

An tambaye shi idan yana da burin kara aure, sai ya kada baki yace, shi aure zuwa yake yi don haka babu wani zabi sai abinda Allah ya tabbatar mana.

Yanzu haka yaran da Allah ya azurta su da su guda hudu ne, akwai Ahmad, Aliyu, Fatima da Habiba.

Rahoto dafa👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button