Advertisement
Labaran Hausa

Ina gargadin masu yada hoton amaryar da zan aura a soshiyal midiya domin haramun ne, cewar Aminu Daurawa

Ina gargadin masu yada hoton amaryar da zan aura a soshiyal midiya domin haramun ne, cewar Aminu Daurawa

Daga jiya zuwa yau hoton Amaryar sheikh Aminu lbrahim Daurawa wanda ya karade kafafen sada zumunta sosai.

To shine gidan rediyon Freedom Radio FM dake jihar kano ta samu tattaunawa da malam domin tabbatar da shin da gaske ne wannna maganar auren.

Ita wannan yarinya haulatu Ishaq itace gwarzuwar Kur’ani a Nigeria baki daya ita tazo na daya kuma aka yi mata kyautar wannan.

Wannan shine abinda ya bani sha’awa sabida irin kwazo da himma da wannan hafiza tayi, tayi kokari tazo a gaban malamai a Nigeria dama duniya baki daya yana da kyau mu nuna kimarsu, darajarsu da kuma martabarsu.

Irin manyan malamai atta irai da sauransu ba wanda sunkayi fice a gasar kyau ba.

A cikin zantawar malam ya bada labarin wani ya bashi labarin ya auri hafizar Alkur’ani yau shekarar su ashirin da daya 21 suna da hafizan Alkur’ani guda hudu duk sun harddace Alkur’ani.

A lokaci daya tana karatun boko tana karanta macro biology tana level 300L, Malam ya kara da cewa na auri mata masu ilimi kuma naga amfanin ilimin sosai shi yasa a wajena nafi son mata masu ilimi domin darajarsu.

Wanda ana yi mata kwaliya a dakin babbar ta amma wasu suje sun yada tunda ba wani taro ko biki akayi ba duk wanda ya yada wannan yayada barna da fasadi a bayan kasa.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekkiyar shirar da aka yi da Malamin.

Rahoto daga👉 Hausaloaded

Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button