
Ingancaccan maganin saurin inzali wato saurin kawowa a lokacin saduwa
Ingancaccan maganin saurin inzali wato saurin kawowa a lokacin saduwa
Hanyoyin magance saurin inzali wato saurin kawowa suna da yawa wasu hanyoyin na yiwa wasu aiki wasu kuma sabanin haka.
Don haka ga hanyoyi kamar haka da mutum zai iya jarrabawa domin neman dacewa.
(1) – A nemi citta “ginger” musamman danya sai a wanke a kuma karkare ta sannan a dake ta, sai ayi shayi da ita bayan an tafasa ta a kofinshayi sai a zuba Zuma ta bada dandano a sha shayin da dumi, za’a ana yin wannan hadin safe da rana.
Du wanda yake fama da matsalar saurin inzalin to idan ya dimanci yin wannan hadin da muka kawo muku, hakan zai kara masa karfin gaba da kuma jinkirin kawowa a lokacin da yake saduwa da iyalin sa.
(2) – A nemi man na’a-na’a mai kyau a wanke gaba da ruwan dumi a goge lemar sannan sai a shafa man a mazakutar ya shiga fata amma banda kofar fitsari.
Idan zakari yana mike sai a jira bayan minti 10 zuwa 15 sannan sai a fara saduwa da iyali.
Man na’a-na’a na rage kaifin dandano da azzakari keji ta yanda zai hana saurin kawowa lokacin jima’i, haka kuma za’a iya amfani da man kanimfari mai kyau a maimakon man na’a-na’a.
(3) – Fita daga gaban mace na ‘yan mintoci a lokacin da mutum yaji ya kusa kawowa da kuma fita daga cikin farji da matse kan azzakari da hannu a lokacin da mutum yake akan hanyar kawowa, shima yana hana saurin inzali.
(4) – Bayan kawowar farko, kawowa ta biyu na zuwa da lokaci mai tsawo kafin mutum ya sake fitar da wani maniyyin a karo na biyu.
Don haka idan mutum yana son ya dade bai yi inzali ba to ya tari jima’i a karo na biyu wanda zai bashi lokaci mai tsawo kafin yayiinzali.