Advertisement
Labaran Hausa
Trending

Jamila Ibrahim Ta Bayyana Dalilan Da Yasa Bai Kamata Ace Amare Suna Kishi Ko Gasa Da Uwargida Ba

Jamila Ibrahim Ta Bayyana Dalilan Da Yasa Bai Kamata Ace Amare Suna Kishi Ko Gasa Da Uwargida Ba

Shaharariyar mai amfani da kafar sada zumunta ta facebook Jamila Ibrahim ta bayyana cewa ba daidai bane amare su rika yin kishi ko gasa da uwargida a gidajen mazajen su ba domin kuwa ita tasha wahalar mijin.

Jamila wacce ita ce keda dandalin Faccbook na home of Solace ta bayyana haka ne a wani rubutu data wallafa a shafinta da safiyar Lahadin nan.

Tace tana mamakin yadda wasu amaren ke yi na yanda suke kokarin nuna kishi da gasa da uwargida wacce su zuwa suka yi suka tarar da ita da mijin, ba tare da sun san irin fadi tashin da ta sha tare da shi ba.

Ta kara da cewar bai kamata amarya ta rika cewa duk abinda miji yayi ma uwargida wai itama dole san an yi mata ba.

Ina mamakin wasu amare da suka je suka sami uwargida da mijinta da sukayi aure tun baida komai sannan su dinga kishi da ita dan miji yafi kashe mata kudi.

Wasu ma harda cowa duk abunda za’awa uwargida sai dai ayi masu iri daya.

Naga wacce ma tazo ta sami uwargida da jecp tace lallai sai dai miji ya siya mata irin na uwargidan.

Malama ke da kika zo jiya jiya har akiyi graduating daga nursery ki shiga university, a Ina aka taba hakan? inji Jamila Ibrahim.

Komai a hankali ake bin shi Jamila ta janyo hankulan mata musamman ma dai amare da kuma wadanda ke shirin auren mijin da yake da wata matar kafin su akan su sani cewa komai sannu a hankali ake bin shi ba tare da yin gaggawa ba tunda basu san irin gwagwarmayar da aka sha kafin ta zo ba.

Ta kara da cewar kada amarya ta dauka wai ko don miji baya son uwargida ne ko kuma wai don ya gaji da uwargidan ne ya aurota, tace ba haka bane, iyaka dai mijin yana kokarin cika umarnin Ubangiji ne.

Komai gradual process ne, baa komai da gaggawa, abunda Kai bakaso ayi Maka Kar kayiwa wani , bakisan irin gwagwarmaya da sukayi tare ba, bakisan wani irin rayuwa sukayi ba ke kinzo kin samesu kina son kiyi gasa da ita.

An auro uwargida don cika umarnin Ubangiji ne.

An auro uwargida don cika umarnin Ubangiji ne

Ba wai baya sonta ne ya auro ki ba, ba wai ya gaji da ita bane ya auro ki, ya auro ki ne Dan cika umarnin Allah da manzon sa.

Daga karshe dai ta ja hankalin amaren akan su kasance masu hakuri da biyayya ga mazajen su ba wai ya zamto suna gasa ko rigima da uwargida ba.

Don haka kowacce amarya ta natsu ta
kama kanta har layi ya biyo ta kanta, iya biyayyar ki iya kulawa da zaki samu cikin kwanciyar hankali, ba wai gasa da rigimar zaisa ayi maki abunda kikeso ba.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button