
Jaruma Momee Gombe tayi magana kan yarinyar da ake cece-kucen cewa ita ta haife ta
Jaruma Momee Gombe tayi magana kan yarinyar da ake cece-kucen cewa ita ta haife ta
A karon farko jarumar kannywood Momme Gombe tayi bayani kan cece- kucen da ake tayi na cewa ta taba haihuwar yarinya ‘yar kimanin shekaru goma sha biyu.
Cikin satin nan ne dai wani bidiyo ke ta yawo a kafan sada zumunta na wata yarinyar ‘yar kimanin shekaru goma sha daya.
Inda wani matashi ya titsiyeta a wani shago yarinyar ke bayanin cewa ita ‘yar cikin Momme Gombe ce, hakan ne yasa mutane suka yi ca kan shi wannan matashin.
Inda wasu ke cewa shi menene nashi wata riba ya samu da har ya dakko yarinyar yake nunawa duniya.
Inda wasu kuma ke cewa yayi dai-dai da yayi haka sakamakon ita ta boyewa duniya cewa ta taba haihuwa, wasu kuma na cewa ai koda haihuwar ne Momme Gomben ta cancanta ta haife yarinya kamar wannan, domin ai ta hanyar sunnah aka haifeta bata hanyar banza ba.
Zuwa yanzun dai jaruma Momme Gomben ta fito tayi bayani inda ta tabbatar da cewa ita fa bata da alaka na kusa ko nesa da wannan yarinyar da ake ta yadata a duniya, hasali ma bata taba ganin yarinyar ba.
Inda ma jarumar take cewa: Na taba aure amma kuma ban taba haihuwa ba duniya ma ta san da Haka.
Inda ta kara da cewa, idan ma shi matashin da yayi wannan abu yayi ne da wani manufa, toh Allah ya saka mata.
Ga cikekkiyar bidiyon a kasa domin ku kalla.