
Jaruma Zakiyya Ibrashim ta bayyana irin alkairin da take samu tunda tabar shirin fim ta koma mawakiya
Jaruma Zakiyya Ibrashim ta bayyana irin alkairin da take samu tunda tabar shirin fim ta koma mawakiya
Tsohuwar jaruma a Masana’antar Kannywood “Hajiya Zakiyya Ibrahim” ta bayyana cewa, tana samun alheri bakin gwargwado tun daga lokacin data koma cin tudu biyu, wato ta rikide daga jarima ta koma mawakiya.
Ya zuwa yanzu dai tayi wakokin siyasa masu yawa inda tafi samun kudi, ban da na yabon Manzon Allah (S.A.W.) dana soyayya wadanda suma tayi su da dama.
Haka kuma jarumar, wadda ta dade ana damawa da ita a Kannywood furodusa ce wadda ta shirya fina-finai masu yawa nata na kan ta.
A tattaunawar da mujallar Fim tayi da ita Zakiyya tace: Kamar yadda na dade ina yin fim a matsayi na na jaruma, kuma haka na dade ina daukar nauyin shirya fim.
To ita ma wakar haka na dade da ita, ta cigaba da cewa tun a shekarar 2008 na fara waka lokacin da aka bude ‘Hikima’.
Don ba zan manta ba, a lokacin ne Sani Lawan Kofar Mata ya sa Aminu Ala yayi album na wakokin Malam Shekarau.
To ina cikin wadanda suka yi amshin wakar kuma tun daga wannan lokacin sai na fara tunanin yadda zan fara shirya tawa ta kai na, don ka san a lokacin masana’antar ta shiga wani hali.
Don haka sai na fara da wakar yabon Manzon Allah (S.A.W) wadda na bayar aka rubuta mini.
Kuma daga nan sai na shiga wakokin fim har na rika sayarwa wasu kuma ina yin amfani dasu a cikin fina-finan dana dauki nauyin su, kamar wakokin da suke cikin fim din “Yar Asali” duk ni na yi su.
To dahaka dai na fara har na zama mawakiya.
Dangane da wakokin da tafi yi a yanzu kuwa Zakiyya tace: A gaskiya tun daga shekarar 2019 nafi mayar da hankali na a kan wakokin siyasa, sabida sune zaka yi a biya ka tunda yanzu babu kasuwar sidi, to a haka na yi wa ‘yan siyasa masu yawa waka da gwamnoni da ‘yan majalisa.
Sannan kuma na bude shafi na na YouTube ina saka wakokin da nake yi, don haka ina samun cigaba sosai.
Zakiyya wadda a Kano take da zama taja hankalin abokan sana’ar ta dasu guji abin da zai rika jawo masu magana, sannan sukuma jama’a su daina kallon ‘yan fim a matsayin lalatattu.
Domin duk wanda kaga yana yin wani abu da bai dace ba to da man can tun a gidansu lalatacce ne, mu ‘yan fim muna da tarbiyya, inji ta.
Rahoto daga👉 Fim Magazine