Advertisement
Labaran Hausa

Jarumar kannywood Rukayya Dawayya ta bude katafaren wajan gyaran jiki na Mata a Kano

Jarumar kannywood Rukayya Dawayya ta bude katafaren wajan gyaran jiki na Mata a Kano

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Rukayya Umar Santa wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya, ta bude katafaren gurin gyaran jiki na mata a Kano.

Mutane da dama sun halarci bikin bude gurin Bikin kaddamar da wannan guri data bude, inda ya samu halarta mutane da dama daga ciki da wajen masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood wadanda suka zo don taya murna da kuma yin fatan alkhairi ga jarumar.

Jaruma Dawayya dai ta kaddamar da wannan katafaren guri ne dai data sanya ma suna “DY Utrat 85” a ranar Laraba 26 ga watan Oktoban nan da muke ciki, a titin Guda Albdullahi dake Farm center a birnin Kano, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.

Mahalarta taron da dama sun yaba wa jaruma Dawayya bisa wannan yinkuri data yi.

Haka nan ma mutane da dama sun sayi wasu daga cikin irin kayayyakin da za’a rika saidawa a gurina yayin bikin kaddamar wa.

Daga cikin mahalarta taro akwai irin su Ismail Na’abba Afakallahu, shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano.

Akwai fitaccen jarumi Nura Hussaini, da su Hadizan Saima, Fauziyya Maikyau, Hannatu Bashir, Saratu Gidado, Asma’u Sani da sauran wasu da dama daga ciki da wajen masana’antar ta Kannywood.

Da take jawabi jim kadan bayan kaddamar wa, jaruma Dawayya ta bayyana cewa: dama ita ta dade tana sha’awar samar da gurin gyaran jiki da kuma kwalliyar mata, wanda a yanzu gashi ta cimma burinta.

Tsarin mu ya bambanta da irin na sauran gurare, ta kara da cewa tsarin su ya ban banta da irin na sauran gurare domin sun samar da kayayyaki irin na kasashe daban daban don amfanin mutanenmu.

Dawayya ta kara da cewa, basu tsaya iyaga kayyan kwalliya da gyaran jiki kadai ba, zasu rika hadawa da kayayyakin amfanin yau da kullum na gida.

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar wa, shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Isma’il Na’abba Afakallahu ya yaba da kokarin jaruma Rukayya Dawayya wajen bude irin wannan katataren guri na gyaran jiki.

Afakallahu yace, wannan abun a yaba mata ne duba da yadda tsarin gurin daya kasance ta yanda zai kiyaye mutuncin mata, sannan yaja hankalin mata akan su rika assasa sana’o’in da zasu rika kare mutuncin mata.

Yanzu idan mu ka duba, wannan wajen an tsara shi ne bisa kiyaye mutuncin duk wata mace da zata zo wajen domin ayi mata gyaran jiki, sabida yanayin tsarin wajen, mutum ko shi ya kawo matar sa to sai dai ya ajiye ta ya tafi, don ba ayi wajen don maza ba.

Koda yake akwai wani bangare na gyaran jikin maza, amma dai ba a hade su keba.

Don haka samar da irin wannan waje shi ne zai tabbatar da kiyaye mutuncin mu da na iyalan mu. inji Afakallahu.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button