Advertisement
Labaran Hausa

Jarumar ‘Kwana Casa’in’ Ikilima Yusuf ta yi bikin cika shekara 26 a duniya

Jarumar ‘Kwana Casa’in’ Ikilima Yusuf ta yi bikin cika shekara 26 a duniya

JARUMA a shirin ‘Kwana Casa’in’ na gidan talbijin na Arewa24, Ikilima Yusuf, ta shirya taro na musamman domin cikar ta shekara 26 a duniya.

A ranar Asabar da ta gabata aka yi walimar a Kano, kuma masoya da ‘yan’uwa da abokan arziki da dama sun halarta, irin su Rashida Adamu Abdullahi da Safiya Adam.

Bayan cikin abinci da abin sha na musamman, an kuma yi rawa an cashe har zuwa dare, inda kuma aka rufe taron da yin jawabin godiya ga mahalarta.

A jawabin ta na godiya, Ikilima ta ce, “Na yi farin ciki sosai da masoya na da kuma halarci wannan waje. Lallai kun nuna mini ƙauna kuma kun nuna kuna so na, don haka ina godiya sosai.

“Kuma ina ƙara godiya ta musamman ga babbar yaya ta, shugabar ƙungiyar ‘yan fim mata ta AKAFA, wato Ambasada Rashida Adamu Abdullahi Maisa’a. Ina fatan Allah ya kai kowa gidan sa lafiya.”

Kalli Hotunan Anan

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button