
Jarumar Ladidi Fagge Ta Bayyana Cewar Bata Da Masaniya Akan Mugayen Labaran Da Ake Yadawa Akanta
Jarumar Ladidi Fagge Ta Bayyana Cewar Bata Da Masaniya Akan Mugayen Labaran Da Ake Yadawa Akanta
Dattijuwar jaruma a masana’antar Kannywood, Hajiya Ladidi Fagge ta shaida cewa ba ta da masaniya dangane da labari mara dadin da ake ta yadawa dangane da ita.
A kwanakin baya labari ya bazu a kafafen sada zumunta wanda aka dinga cewa ba ta da lafiya, wasu su na ta cewa tana mawuyacin yanayi kwance a gadon asibiti tare da yada wasu hotunan da tayi rama kwarai.
Akwai wadanda su ka dinga cewa ma ta rasu. Wannan dalilin ne ya sanya Mujallar Fim ta nemi tattaunawa da ita don jin gaskiyar abinda ke faruwa saboda waka a bakin mai ita ta fi dadi.
Yayin da aka tambayeta akan rashin lafiyarta ta bayyana cewa:
“Tabbas a baya na yi rashin lafiya, amma gaskiya ba yanzu bane. Tun a watannin baya ne. Na kuma samu sauki na ci gaba da harkoki na. Maganar da ake yi yanzu haka anjima kadan zan wuce yin fim din Alaqa a anguwar Maidile.
Kwanakin baya gidan rediyon Arewa su ka kira ni su na tambayata dangane da labarin ba na da lafiya kuma wai ina neman taimako na kudi da addu’a.
“Sai na shaida musu cewa ban fada wa kowa cewa ina neman taimako ba, amma idan za a bani wani abu na taimako ba zan ki amsa ba.
“Kuma batun ina neman addu’a ai ba sai mutum yana kwance zai nema ba. Ina bukatar addu’a wurin masoya na a yanzu da kuma ko wanne lokaci.”
Jarumar ta yi fatan alheri ga masoyanta da kuma yadda su ka nuna damuwarsu akan halin da take ciki, har su ke tunanin tana mawuyacin yanayi.
Kamar yadda ta bayyana, Rikadawa ne ya sanya mata suna Ladi Tubless wanda yanzu haka ta yi fice da shi a masana’antar Kannywood.
Ta ce kaddara ce ta kawo ta masana’antar musamman ganin cewa idan har Allah ya yi sai ka ci abinci a wuri to babu shakka hakan sai ya tabbata.
Ta bayyana yadda ta fara shirin fim tun daga makaranta lokacin ana hada ‘yan shirye-shirye har Ubangiji ya yi zata ci abinci da harkar.
Yayin da aka tambayeta fim din da tafi so, ta ce duk fina-finanta tana matukar son su musamman wadanda ta kashe kudadenta wurin shirya su da kuma wadanda aka nemi ta yi su saboda ta karu kuma tana matukar alfahari da su.
Ta kuma hori matasa na masana’antar da su kasance masu neman ilimi ko da kuwa ba neman aiki za su yi da shi ba saboda akwai lokacin da zai zo wanda in har babu ilimi ba za a yi da mutum ba.
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.