
Jarumar shirin kwana casa’in Rayya ta kammala karatunta na jami’a
Jarumar shirin kwana casa'in Rayya ta kammala karatunta na jami'a
Fitacciyar jaruma Surayya Aminu wacce aka fi sani da Rayya a cikin shirin Kwana Casa’in mai dogon zango, ta kammala karatunta a makarantar jami’a Kamar yadda rahotanni suka nuna.
Ko da take shirin fim din, hakan bai karkatar da ita daga karatunta ba, sai da ta zage damtse ta kammala.
Jarumar ta wallata hotunanta a shafinta na sada zumunta instagram cike da farin ciki yayin da ta gama rubuta jarabawar karshe da abokan karatunta, sanye da farar riga wacce aka yi mata rubutu kala daban-daban a jikinta wanda ake kira da “sign out”.
Nan da nan masoyanta da masu yi mata fatan alkhairi suka dinga kora mata addu’o’i na fatan alkhairi, yayin da wasu suka dinga mamakin ganin yadda ta hada karatu da sana’ar fima lokaci guda.
Da alamu Foliteknik din jihar Kano ta kammala don kowa ya san a halin yanzu jami’o’in gwamnati basu dade da komawa yajin aiki ba, yayin da na kudi kuma ba yanzu bane lokacin gamawarsu ba.
Sannan a shafin nata ta bayyana cewa, a Kano ne ta kammala karatun wanda duk wanda yake da labari zai gane cewa ‘yan foliteknik ne suke gama karatu yanzu.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa