Advertisement
Labaran Hausa

Jarumi Adam A Zango ya nuna alhininsa kan rasuwar dan wasan barkwanci Kamal Aboki

Jarumi Adam A Zango ya nuna alhininsa kan rasuwar dan wasan barkwanci Kamal Aboki

Har yanzu dai wasu daga cikin jaruman kannywood suna cigaba da nuna alhinin su akan rasuwar dan wasan barkwanci Kamal Aboki, wanda a yanzu muka samu wata wallafa daga shafin jarumi Adam A Zango na Instagram yana nuna alhinin rasuwar Kamal Aboki.

Adam A Zango dai ya wallafa hoton marigayi Kamal Aboki a shafin nasa na Instagram tare da rubuta cewa, Allah ya gafarta maka Kamal Aboki.

Mabiyan jarumi Adam A Zango da dama sun yiwa marigayi Kamal Aboki addu’o’i da nema masa gafarar Ubangiji.

Muma a namu bangaren muna rokon Allah ya gafarta masa ya masa rahama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button