Advertisement
Labaran Hausa

Jarumi Ali Nuhu ya maka Hannatu Bashir a kotu bisa zargin cin mutuncin da tayi masa

Jarumi Ali Nuhu ya maka Hannatu Bashir a kotu bisa zargin cin mutuncin da tayi masa

Fitaccen jarumin Kannywood “Ali Nuhu” ya kai karar jaruma kuma furodusa a masana’antar “Hannatu Bashir” gaban alkali bayan zarginta daci masa mutunci ta hanyar tura masa sakon kunshe da kalaman cin mutunci.

Salima Muhammad Sabo lauyar Ali Nuhu ta ofishin lauyoyi na M.L. Ibrahim and Co, ta shigar karar ne a kotun majistare dake lamba 58 a anguwar Noman sland cikin Kano.

Mujallar Fim ta gano yadda Ali Nuhu yayi karata sabida ba’a samu abin da ake nema ba a wani fim din Hannatu wanda aka yi alkawari da jarumin kuma ya saba.

Kamar yadda bayanai suka nuna, an yi alkawari da Ali Nuhu cewa za’a dauki fim din ranar 10 ga watan Oktoba amma bai je wurin ba kasancewar yayi wata tafiya.

Rashin zuwan nasa yasa wajibi aka dage daukar bangaren aikin zuwa washegari, kuma a ranar ma bai samu zuwa ba, ta bayyana cewa ba zai samu zuwa ba sai ranar gaba.

Wannan lamarin ya hassala Hannatu inda ta tura masa sako ta waya tana cewa, ba ta bukatar aiki da shi.

Wannan sakon ne yasa jarumin yaji haushi inda yace masa tayi masa rashin kunya sannan sai ya dauki matakin shari’ar a kanta, ita kuma tace tana jiran sa.

A takardar wacce lauyar sa ta shigar, Ali Nuhu ya shaida cewa Hannatu tayi masa munanan kalamai har da cewa ya zalinceta.

A cewar sa, babu wata sa hannu da suka yi da ita cewa zai yi mata fim kuma huldar kasuwanci ce ta hada su amma kuma a haka sai da ta tura masa maganganu na batanci tare da zubar masa da kima a idon jama’a.

Hakan yasa ya gabatar da karar sa domin kotu ta kwatar masa hakkinsa, ya dauki hoton tes din data masa inda ya makala da takardar karar domin kotu ya gani.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button