
Jarumin Kannywood Hannifi Rabiu’ Musa Dan Ibro Yaci Gasar Mota
Jarumin Kannywood Hannifi Rabiu' Musa Dan Ibro Yaci Gasar Mota
A SAKAMAKON gasar ‘Sha’aban Sharaɗa Challenge’ da aka fitar shekaranjiya Asabar, jarumin Kannywood Hannafi Rabilu Musa Ɗan Ibro ya samu shiga sahun waɗanda su ka yi nasarar cin kyautar mota da kuma kuɗin mai N100,000.
Ita dai wannan gasa, mawaƙi Dauda Rarara ne ya shirya ta domin tallata wa ɗan takarar zama gwamnan Jihar Kano Sha’aban Ibrahim Sharaɗa. A gasar, an haɗa ‘yan fim da mawaƙan Kannywood da na yabon Annabi, wanda hakan ya sa aka samar da zakara a kowanne rukuni.
Hannafi ya shiga gasar ne a matsayin ɗan wasan barkwanci, kuma sai ya kasance shi ne ya zo na ɗaya.
Kusan shekara biyu kenan da shigar Hannafi harkar fim a ɓangaren wasan barkwanci wanda hakan ya sa ake ganin zai maye gurbin mahaifin sa, marigayi Rabilu Musa Ɗanlasan (Ibro).
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.