Advertisement
Labaran Hausa

Jarumin Kannywood Yusuf Sasen(Lukman Labarina) Zai Angwance Da Amaryarsa Amina

Jarumin Kannywood Yusuf Sasen(Lukman Labarina) Zai Angwance Da Amaryarsa Amina

JARUMI a Kannywood, Yusuf M. Abdullahi (Saseen) zai angwance a ranar Asabar mai zuwa, 24 ga Disamba, 2022.

Jarumin na ci gaba da raba katin gayyatar bikin auren a soshiyal midiya.

Kamar yadda katin ya nuna, za a daura auren Saseen da masoyiyar, Armina Zakari Yunusa Daya, a gidan Makaman Fika, da ke layin makaranta a garin Potiskum cikin Jihar Yobe.

Bugu da kari, a daren ranar Lahadi aka bude shagalin bikin da wasan kwallon kafa da aka buga tsakanin kungiyoyi biyu, Kannywood’ da Saseen Friends Team’. An buga wasan a filin wasa na Dan Nagari da ke Sultan Road a Kano.

Bayan daurin aure ran Asabar, a ranar Lahadi kuma za a yi walima.

Sai dai kuma har zuwa yanzu ba a ga hotunan kafin aure (pre-wedding pictures) ba, kar yadda sauran jarumai ke yi.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa Saseen shi ne Lukman, saurayin Sumayya a cikin shirin Labari Na, mai dogon zango na darakta Malam Aminu Saira.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button