
Kada jahilin da ya sake suka na akan ina bin bayan Rarara domin ni babban Lakcara ne, cewar jarumi Ahalan
Kada jahilin da ya sake suka na akan ina bin bayan Rarara domin ni babban Lakcara ne, cewar jarumi Ahalan
Tsohon jarumin Kannyvwood, Aminu Ahalan ya bayyana a wani bidiyo daya saki a shafinsa na TikTok, inda ya dinga surutai yana zage-zage game da masu sukarsa akan yabon mawaki Rarara da hawa wakarsa da yake yi.
Ya fara da cewa: Salam wannan bidiyon naku ne musamman marasa kunyar nan naTikTok, abinda nake so in gaya muku, duk cikin ku babu wanda ya isa gajojin banza da na wofi.
A cewarsa, ya kula da ‘yan bani na iya da kuma wawayen dake kafafen sada zumunta da suke caccakarsa da zarar ya yabi Rarara, kuma a yace ba ya neman komai a wurin mawakin.
A cewarsa, Rarara yana kokari kwarai wurin kyautata wa jama’a kuma shi din ba jahili bane, don lakcara ne a jamia.
Ya ja kunnen jama’a inda yace shi da babban mutum ne, kada aga yana harka a soshiyal midiya tare da jama’a amma shi din ba karamin mutum bane.
Ya yi zagi masu nauyi ga duk masu sukarsa inda yace, ya wuce saninsu, kuma su kiyaye shi tunda su jahilai ne marasa kunya da mutunci.
Ya cigaba da cewa: Akan mawaki Rarara zanci uwarkowa banzaye jahilai Ass holes, tunda baku da hankali, bari nima in yi alfahari nii lakcara ne nafi karfinku.
Kuma Rarara yafi karfinki, ban yi wa ministoci ko sanatoci roko bane zan yi wa Rarara?, ni dai kawai ina son shi ne kuma ayyukan da yake yi suna burge ni, don haka ku jahilai ne kma ba ta taku nake yi ba.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa
Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.