
Kan dukan malamar islamiyya: kullalliya ‘yan unguwar mu suka shiryamin, cewar Baba Ari
Kan dukan malamar islamiyya: kullalliya 'yan unguwar mu suka shiryamin, cewar Baba Ari
Jarumin barkwanci Malam Aminu Baba Ari ya bayyana cewa, dukan malamar makarantar islamiyya da ake zargin sa da aikatawa wata kullalliya ce wasu gungun mutane suka kitsa a unguwar su, kamar yadda “Fim Magazine” suka ruwaito.
Yace, bai san abin da ya sa suka tsane shi ba, Baba Ari ya fadi haka ne a lokacin da yake karin bayani kan labarin cewa ya doki malamar makarantar islamiyyar da ‘yar sa ke halarta har ta suma.
Idan kun tuna, mujallar Fim ce ta soma wallafa labarin, bisa wani bincike da tayi kan zargin da ake masa.
A labarin wanda muka wallafa a ranar 6 ga watan Oktoba 2022, mun ruwaito wata malamar makarantar islamiyya dake unguwar Mubi, kusa da Kofar Nassarawa a cikin birnin Kano, ta zargi Baba Ari dayi mata dukan tsiya kuma ya yi barazanar zai taka ta da takalmi.
Malamar mai suna Zainab ta shaida wamu jallar Fim cewa, wasu yaran makarantar ne suke karatu, a cikin su har da ‘yar Aminu Baba Ari, inda suka yi laifin da za’a hukunta su.
To amma kuma da hukuncin yazo kan ‘yar Baba Arin sai ta rike bulalar ta hana a dake ta, a yunkurin dukan ta ne har ta fadi kasa aka ce aljannun ta ne suka tashi.
Zainab tace: Bayan ta Aminu Baba Ari ya
samu labarin sai yazo ya rufe ni da duka har na fadi kasa, sannan ya yi kokarin taka ni da takalmin sa.
A lokacin Baba Ari yace bai yi mata irin dukan da ake cewa ya yi din ba illa iya ka ya daki dankwalin ta baya ne.
A karin bayanin sa kan labarin, Baba Ari ya fadawa mujallar Fim cewa, akwai karya a labarin da ake yadawa.
Yace, duk da dai na dan yi magana a baya amma a yanzu ina so nayi maka bayanin yadda abin ya faru tun da farko sabida naji yadda ake ta yada labarai na karya a kai na.
Ina ganin labarai kala-kala wasu suce na yi mata dukan da na sumar da ita, wasu suce na karya ta da sauran labarai na karya.
To a gaskiya abin da ya faru ni ban san wannan yarinya malamar islamiyyar ba ce, domin kawar ‘yar ta ce ita wadda aka daka din.
Nazo gida na zauna ina cin abinci sai aka sanar da ni ana fada da ‘yar ta Aisha a makarantar, don haka sai nayi sauri na fita naje makarantar.
Kuma ina zuwa sai ga wannan yarinya rike da bulala tana dukan ta har ta kum bura mata gefen ido.
Wannan ya sa na bi wannan yarinya na buge ta ta baya don ta daina, kuma tabbas na san na bugi gefen mayafin ta.
Amma ban yi mata dukan da ake cewa na yi mata dukan tsiya na sumar da ita na taka ta da takalmi ba.
Kuma ni ban yi zaton ta na a matsayin malamar islamiyyar ba ce, na zata fadan su ne na yara idan malamai basa kusa.
Baba Ari yace, wata makarkashiya ce aka kulla domin a bata masa suna, kuma ‘yan banga runguwar sune suka kitsa maganar.
Yace, to amma duk bayan an yi magana an gama sai ‘yan bijilanti na unguwa suka shigo harkar sabida suna da wata kullalliya da ni, don haka suka kira ‘yan jarida suka tsara mata abinda zata fada tare da kai maganar ga kungiyar kare hakkin dan adam, wai dai su bata mini suna.
Wannan ya sa aka je ofishin ‘yan sanda na Kwalli da uban yarinyar aka kashe magana.
Dan wasan yace, ba tun yau ba ne ‘yan bangar unguwar tasu suka kafa masa kahon zuka, kuma bai san dalili ba.
Yace, ni ban san abin da nayi wa su ‘yan bijilantin unguwar mu ba suka tsane ni, sabida sun yi ta kokarin yi mini haka a baya basu samu hanya ba sabida ina zaune da kowa lafiya.
Gawani nan da aka kama ya doki matar aure har gida basu yi komai ba, an samu wani yana luwadi basu yi komai ba, ga masu laifuka nan.
Don ko mai unguwar mu da ya ji maganar ya ce abin ya ba shi mamaki, don ba na fada da kowa.
Kuma ita wannan makarantar islamiyya ina cikin masu ba ta gudun mawa, don a satin da ya wuce makarantar ta bani takardar karramawa a taron data shirya don karrama masu bata gudunmawa.
Sabida haka, wasu ne dai da suke da wata manufa da ni suka shirya yada labarin don a bata mini suna, amma kowa ya san ba ni da rigima a unguwar mu ko a wajen harkar fim dana ke yi.
Rahoto daga👉 Fim Magazine