Advertisement
Labaran Hausa

Kotu A Jihar Kano Ta Yankewa Abduljabar Kabara Hukunchi Kisa Ta Hanyar Rataya

Kotu A Jihar Kano Ta Yankewa Abduljabar Kabara Hukunchi Kisa Ta Hanyar Rataya

Yanzunan Majiyarmu Ta Samu Labari Daga Shafin Bbc Hausa Dake Nuni Da Cewar An Yake Hukunchi Kisa Ta Hanyar Rataya Ga Abduljabar Nasiru Kabara Kamar Yadda Aka Wallafa

Babbar kotun shari’ar Musulunci ta jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laiñi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad.

An yanke hukuncin ne a ranar Alhamis bayan da Mai Sharia lbrahim Sarki Yola ya ce an same da dukkan laifukan da ake tuhumarsa da su.

Daga cikin tuhumar da ake masa, hadda zargin waazinsa zai iya tayar da tarzoma a jihar Kano.

Bayan an same shi da laifukan, sai Mai Shari’a Sarki Yola ya dage zaman kotun don ba shi damar rubuta hukuncin da za a yanke wa malamin

Bayan dan lokaci kuma sai aka koma zaman kotun tare da yanke hukuncin.

Sai dai kafin a tafi hutun Sheikh Abduljabar siru Kabara ya yi magana ta karshe inda ya ce lauyan da ke kareshi bai san shi ba kuma baya neman afuwa saboda a cewarsa bai aikata laifi ba, don haka a gaggauta yanke masa hukunci.

A ranar Juma’a 16 ga watan Yulin 2021 ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin batanci ga addini da kuma tunzura jamaa, zargin da ya sha musantawa.

Za mu ci gaba da kawo muku karin bayani.

Source of Bbc Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button