Advertisement
Labaran Hausa

Kotu ta aike da Murja Ibrashim Kunya gidan Yari

Kotu ta aike da Murja Ibrashim Kunya gidan Yari

Yanzu nan majiyarmu ta samu labarin cewa, wata koyu dake jihar kano ta aiki da Murya Ibrahim kunya shahararriyar ‘yar Tiktok din nan gidan gyaran hali, kamar yadda shafin Hausaloaded suka wallafa.

Kotun shari’ar Muslunci dake Filin Hoki a Kano karkashin mai Shari’a Abdullahi Halliru ta aike da ‘yar Tiktok din nan Murja Ibrahim Kunya zuwa gidan yari.

Lauya Barrister Lamido Abba Soron dinki ya karanto mata kunshin tuhume-tuhumen da ake mata wanda ta musanta.

Ana zargin Murja da bata suna da barazana ga Aisha Najamu ta Izzar So da kuma Ashiru Idris wanda dukanninsu abokananta ne.

Kotun ta dage sauraron karar zuwa 16 ga watan Fabrairun da muke ciki, sai dai Lauyan Murja Barrister Yasir Musa ya nemi a tura ta zuwa Hisbah maimakon gidan Yari sai dai Kotun bata amince ba.

Source of Hausaloaded

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button