Labaran Hausa

Kotu Ta Bada Umarnin A Bulale Wasu Masu Wasan Barkwanchin A TikTok Bisa Laifin Bata Sunan Gandujai

Kotu Ta Bada Umarnin A Bulale Wasu Masu Wasan Barkwanchin A TikTok Bisa Laifin Bata Sunan Gandujai

Kotu ta bayar da umurnin a bulale wasu masu barkwanci a TikTok a Kano, Mubarak Muhammad da Nazifi Muhammad, bisa zargin bata sunan gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje.

Kotun ta bayar da wannan umurnin ne a ranar Litinin 7 ga watan Nuwamban 2022, bayan taurarin na TikTok sun zargi Ganduje da cin hanci. Jaridar L.egit.g ta rahoto.

An dai cafke masu barkwancin ne sannan aka tura su zuwa kotu bayan wani bidiyon su na TikTok ya bayyana inda suke zargin Ganduje da cin hanci.

An tura su kotun ne bisa tuhumomi guda biyu na bata suna da tada fitintinu.

A wajen karar, alkalin kotun, Aminu Gabari, ya bayar da umurnin a yiwa kowane daga cikin su bulala 20 sannan kuma ya sanya su sharar harabar kotun har na tsawon kwana 30.

Kotun ta kuma umurci masu barkwancin na TikKTok da kowanen su biya tarar N10,000.

Ana kammala yanke hukuncin, wani ma’aikacin kotun ya dauko bulala ya yiwa kowanen su guda ashirin.

An dai bulale su ne a bainar jama’a ciki har da wasu yan TikTok din da suka zo kotun domin nuna musu goyon baya.

Alkalin yace yana fatan cewa hukuncin zai zama izna ga saura wadanda ke amfani da kafafen sada zumunta sannan ya tabbatar cewa sun yi takatsantsan da kuma girmama manya.

Lauyan gwamnatin jihar, Wada Wada, yace ya gamsu da hukuncin inda ya kara da cewa yana fatan abinda ya faru ga yan TikTok din ya zama darasi ga sauran mutane

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button