Advertisement
Labaran Hausa

Kotu ta bayar da umarnin dole sai jaruma Hannatu Bashir ta gurfana a gabanta

Kotu ta bayar da umarnin dole sai jaruma Hannatu Bashir ta gurfana a gabanta

Har yanzu dai tsugunne bata kare ba game da rikicin da ya barke tsakanin jarumi Ali Nuhu da jaruma Hannatu Bashir, wacce har ta kai su ga zuwa gaban kotu.

Wata kotun majistiri mai lamba 58 karkashin mai shari’a Aminu Gabari, ta bayar da umarnin cewa dole jaruma kuma furodusa a masana’antar Kannywood Hannatu Bashir ta gurfana a gaban ta.

Kotun dai ta fara sauraron karar da babban jarumin masana’antar Kannywood Ali Nuhu ya shigar a kan jaruma Hannatu Bashir, dangane da zargin da yake mata na cin zarafin sa, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.

Yayin zaman kotun wanda ya gudana a ranar Talata, lauyoyin mai kara da lauyoyin wacce ake kara sun bayyana a gaban kotun, inda suka bukaci kotun da ta amince musu su je suyi sasanci.

Sai dai kotun taki amincewa da wannan bukatar tasu inda ta bayar da umurnin dole wacce aka yi kara, wato Hannatu Bashir ta bayyana a gaban Kotu.

Kotun ta sanya ranar 25 ga wannan watan na Oktoban da muke ciki, domin cigaba da gudanar da shari’ar.

Jarumi Ali Nuhu ya yi karar jaruma Hannatu Bashir bisa zargin taci zarafinsa, zargin da jarumar ta musanta, inda tace abin dake tsakanin su shi ne sakon da ta aika masa kan gazawar sa na cika alkawarin zuwa fara daukar film dinta.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button