
Kotu ta garkame Mubarak Uniquapikin bisa cin zarafin Gwamna Abdullahi Ganduje
Kotu ta garkame Mubarak Uniquapikin bisa cin zarafin Gwamna Abdullahi Ganduje
Kotun Majistiri mai lamba 58 dake Noman sland a Kano ta aike da wasu matasa masu wasan barkwanci zuwa gidan yari.
An gurfanar da matasan ‘yan wasan Barkwancin Mubarak Muhammad da aka fi sani da Uniquepikin da mai ja masa baki Nazifi Isah Muhammad a gaban Kotun bisa zarge-zarge guda hudu.
Hukumar tace fina-finai ta Kano ce ta yi kararsu bisa zargin hada kai da bata suna da cin zarafin Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, tare da yunkurin tayar da hayaniya a wani faifan bidiyo da suka fitar.
Yayin zaman Kotun a ranar Laraba wadanda ake zargin sun amsa tuhumar da ake musu, Lauyan dake kare su da iyayensu sun roki kotu da ta yi musu afuwa.
A nan ne kuma alkalin Kotun mai shari’a Aminu Gabari ya dage shari’ar zuwa ranar Litinin 7 ga watan Nuwamban da muke ciki, kamar tadda shafin “Hausaloaded” suka ruwaito.
Fitaccen mai wasan barkwancin nan a manhahar Tik tok “Mubarak Unique Pikin” ya shiga komar Gwamnatin jihar Kano, domin yanzu haka yana gidan dan kande a tsare bayan zagin tsamar nama da ya yiwa Gwamnan jihar na Kano tare da iyalansa baki daya.
Ga duk mai bibiyar dandalin yasan Mubarak da kuma irin Shirin sa da yake yi tare da Kaninsa wanda yake kira da Na’ibi, hankalin ‘yan TikTok ya tashi bayan kama Mubarak.
Bayan Mubarak din yana tsare a wajen hukuma dubban ‘yan uwa da Abokan arziki ne suka dinga taya jaje tare da mika kokon bara zuwa Gwamnan na jihar ta Kano, domin yayi masa afuwa sannan a sako musu dan uwa.
Cikin wadanda suka mika kokon barar sun hada da manyan abokan sa a sahar irin su Baddo “Ali Nuraddeen” Murja Ibrahim Kunya, MJ Talent, Abba C Sale da dai sauran su.
Rahoto daga👉 Hausaloaded