Labaran Hausa

Kotu ta raba auren wani magidanci da matar sa dalilin rashin haihuwa

Kotu ta raba auren wani magidanci da matar sa dalilin rashin haihuwa

Wata kotu dake zamanta a Nyanya dake babban birnin tarayya Abuja ta raba aure na tsawon shekaru goma tsakanin wani magidanci mai suna “Simon” da kuma matar sa mai suna “Blessing Ameh”, a kan dalilin rashin haihuwa.

Kamar yadda “Labarun Hausa” ta tattaro rahoton, ta wallafa a shafinta cewa, Aalkali mai shari’a “Doocivir Yawe” ya raba aure tsakanin wani magidanci da matar sa, bisa dalilin cewa duka mata da mijin sun gaji da cigaba da kasancewa a tare.

Doocivir yace, duka bangaren guda biyu sun aminta da a raba auren kuma harma wanda aka yi kara wato maigidan ya bukaci kotu data cika wa matar sa burinta na rabuwar auren.

A dalilin hakan, kotu bata da wani zabi face ta cika ma mai karar burinta na rokon a raba auren, sabida haka kotu ta rushe auren a cewar Alkalin.

Sannan kotu ta umarci matar data mayar wa maigidan nata kudin sadakin shihar Naira dubu hamsin “N50,000”.

Ma’aikatar jakadancin labarai ta Najeriya ta ruwaito cewa, Ameh ta kai karar Simon kotu ne tana rokon a raba auren nasu a bisa dalilin cewa auran ya fita daga ranta gaba daya.

Na gaji da cigaba da wannan auren, nayi iya bakin kokari na wajen ganin na samu haihuwa amma duk kokarin nawa ya tashi a banza, cewar Ameh.

Nabi tsarin daukar ciki da haihuwa na musamman har sau biyu amma duk da haka ban samu nasara ba, kamar yadda ta shaidawa kotu.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button