Advertisement
Labaran Hausa

Kotu ta sanya ranar da za’a saurari karar da ake yiwa dan china daya kashe Ummita

Kotu ta sanya ranar da za'a saurari karar da ake yiwa dan china daya kashe Ummita

Wata babbar kotun jihar Kano wacce mai shar’a Sanusi Ado Ma’aji ke jagoranta, ta daga sauraron karar da ake yiwa dan kasar Chana “GengQuangrong” wanda ake tuhuma da kisan masoyiyar sa, Ummul kulsum Sani Buhari wacce aka fi sani da Ummita.

Alkalin ya daga sauraron karar ne bisa rashin halartar lauyan dake kare wanda ake tuhumar, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.

A yayin da aka cigaba da sauraron karar a ranar Alhamis “Geng Quangrong” ya roki kotun data daga sauraron karar domin ya samu damar tuntubar lauyan sa domin wakiltar sa.

Da yake mayar da martani Antoni janar na jihar Kano “Musa AbdullahiLawan” bai nuna kin amincewa da bukatar wanda ake kara ba ta a daga sauraron shari’ar.

Lauyan gwamnatin yace: Tabbas ba zamu iya cigaba da wannan shari’ar
ba babu lauya, mai kare wanda ake kara wannan shine tsarin.

A bisa halin da ake ciki mun nemi a daga sauraron karar na dangajeran lokaci domin bada dama ga wanda ake kara ya samo lauya.

Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya daga sauraron karar sai zuwa ranar 4 ga watan Oktoban 2022.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button