
Kotu tayi cafke wata Budurwa data hallaka Saurayinta da wuka bayan wani rikici da suka yi
Kotu tayi cafke wata Budurwa data hallaka Saurayinta da wuka bayan wani rikici da suka yi
Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta
cafke wata matashiya mai suna “Alice Mulak” dake zaune a Unguwar Gwari a karamar hukumar Karu ta jihar, bisa zarginta da dabawa saurayinta wuka a ciki wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan
sandan jihar Nasarawa DSP Ramhan Nansel yace, binciken farkon ya nuna cewa lamarin ya faru ne a bayan Otel din City Rock dake Mararraba da misalin karfe uku da rabi na safe, lokacin da saurayin da budurwar tasa suka samu rashin jituwa a tsakaninsu.
DSP Ramhan Nansel ya kara da cewa, tuni aka kama wadda ake zargin tare da wukar da tayi amfani da ita wajen aikata laifin.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Adesina Soyemi ya bayar da umarnin mayar da wadda ake zargin zuwa sashin gudanar da binciken manyan laifukan kisan kai dake jahar, domin fadada bincike kafin a kai ga gurfanar da ita a kotu don ta fuskanci hukunci.
Rahoto daga👉 Focus News Hausa