Advertisement
Labaran Hausa

Kumatuwa Sun Nuna Kamar Na Matar Auren Gaske A Shirin Fim Din Matar Aure

Kumatuwa Sun Nuna Kamar Na Matar Auren Gaske A Shirin Fim Din Matar Aure

Jarumar Rahama Sadau ta sha caccaka bayan yin wani tsokaci akan sabon shirin fim dinta maI dogon zango mai suna Matar Aure. Kamar yadda ta wallafa a shafinta na Facebook, kumatun da tayi yayin shirya fim din ya sanya ta yi kama da matan auren.

Tabbas babu ko shakka, jarumar ta kara kiba sosai idan aka hada ta akan lokacin da ta fara bayyana a industiri. A lokacin kowa ya san yadda tayi fice a siranta. Sai dai akan ce dare daya Allah kan yi bature, ta yuwu jindadi da samun kudi ne ya sanya ta yin kibar.

Duk da dai akwai wadanda su ke zargin shekarunta sun fara tafiya ne, hakan yasa ta kara kiba kuma ta fito a babbar mace wacce ta dace da shirin Matar aure. Mutane da dama sun yi tsokaci mabambanta a karkashin wallafar da tayi.

Ga wallafar tata:

Tsokacin Al’umma

Ahmad Dauda yace:

Kema Kinyi allura ne domin Kara kiba?”

Wyong Elizabeth Gimba tace:

Kumatu alama ce ta jindadi da kwanciyar hankali, ke ce jarumar da nafi so.”

Maymunah Dabo tace:

Na fara jindadin wannan shirin naku. Ku ci gaba, aiki na kyau.”

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button