Advertisement
Labaran Hausa

Kuskure ne auren ‘yayan talakawa yawancin su ‘yan jari hujja ne, cewar wani uba ga dan sa

Kuskure ne auren 'yayan talakawa yawancin su 'yan jari hujja ne, cewar wani uba ga dan sa

Kada ka auri ‘yar talaka bata san soyayya ba burinta ta kubuta daga talauci, Uba ga dansa.

Wani mutum dan Najeriya ya bayyana shawarar da ya bai wa dansa dangane da aure inda yace kada ya kuskura ya auri diyar talakawa, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwai.

A wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter mutumin yace, yana bayyana hakan ne bisa yadda rayuwa ta koya masa hankali, kuma ya dawo ya gane gaskiya.

Yace, tabbas ‘yayan talakawa ba sa
yin soyayya tsakani da Allah don basu santa ba.

Kamar yadda ya wallafa: Na shawarci da na jiya akan cewa ya kiyaye soyayya da yaran talakawa, bisa yadda na kula da soyayya yawancinsu ba su santa ba kuma basu yarda da ita ba.

Burinsu kawai su kubuce daga mawuyacin yanayin da suka tsinci kawunansu, sannan sune masu ceto ‘yan uwansu daga talauci don su fitar dasu daga fatara

Ba sa godiya akan kananun abubuwa, kullum burinsu ka kara kaimi cewa kana iya yin fiye da haka.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button