
Kamar yadda kuka sani shirin Labarina shiri ne mai dogon zango wanda tashar “Saira Movies” take kawo muku a duk sati.
Shirin Labarina dai yana tattare da kalubale matuka a cikin sa musamman na soyayya, wanda har yanzu an rasa takamemen wanda zai auri Sumayya tsakanin Presdo da Lukman.
Kamar dai yadda aka saba a duk sati kafin a kai ga ranar haska shirin Labarina, ana sakin kadan daga cikin shirin domin masu kallo su san ina za’a dosa kafin a saki gundarin shirin.
A yanzu dai mun kawo muku kadan daga cikin shirin Labarina Season 5 Episode 5 wanda tashar “Saira Movies” ta dora.
Ga kadan daga cikin shirin domin ku kalla.