
Shirin Labarina dai shiri ne wanda ya shahara a fadin Arewacin Nageriya wanda a yanzu haka ba kowane series fim ne ya fishi karbuwa a wajan al’umma masu kallo ba.
A wancan satin daya gabata an tsaya a shirin Labarina kashi na 5 fita ta 6, inda shirin ya kare a dai-dai wajan da Ummi ta fadi bayan Hajiya Babba ta soke baikon da za’a yi musu da Lukman.
A wannan satin kuma tashar “Saira Movies” sun haskaka shirin Labarina kashi na 5 fita ta 7.
Ga bidiyon shirin nan a kasa domin ku kalla.