Advertisement
Magunguna

Maganin karin ruwan maniyyi sadidan ga wanda nasa yayi karanci ko ya tsinke

Maganin karin ruwan maniyyi sadidan ga wanda nasa yayi karanci ko ya tsinke

‘Yan uwa da yawa suna yawan tambaya ta maganin da zai kara musu ruwan maniyyi ga masu karancinsa, ko wadan da nasu ya tsinke.

Insha Allahu ga wata hanya wacce zata taimaka matuka, za’a samu Dabino a bare shi a cire kwallon cikinsa sai a jika shi ya kwana daya, sannan a zuba shi a blender a nika shi sosai.

Sannan a kawo zuma a hada da wannan Dabinon da aka nika a hade su waje guda, amma kar yayi kauri sosai.

Za’a rika shan babban chokali 4 da safe kafin a karya, chokali 4 da yamma haka har tsawon sati 2.

Sannan yawan cin miyar kubewa ma yana
kara ruwan maniyyi, haka nan cin kifi ma yana taimakawa, sannan kuma da motsa jiki ma haka.

Ga kuma yadda Mace zata gyara fuskarta koda kuraje sun fito mata sun bata mata fuska.

Duba da kasantuwar yadda ake duba cikar kyawun mace, fuskarta tana ɗaya daga cikin manya manyan jari da ake la’akari da kuma duba a jikinta. Sannan kuma wani abu da yake ɓata fuskar mace shine ƙuraje.

Kurajen fuska suna sanya muni, da rashin kyawu ga ƴa mace, koda kuwa kyakkyawa ce. Don haka duk wacce ke son kurajen dake fuskarta su ɓace ɓat, ga hanyar da zasu bi.

Kayan haɗin sune ;

Lemon tsami
Kurkur
Zuma

Yadda zaki haɗa :

Mace zata wanke fuskarta sosai da ruwan ɗumi, ta goge da tsumma mai tsafta sannan ta tsaga lemon tsamin gida biyu, ta murje fuskarta dasu (akwai zafi kaɗan). Sai bayan kimanin minti biyar ta tashi ta wanke shi da ruwan dumi.

Sannan ta zuba garin kurkur din nan rabin cokali a cikin zuma cokali biyu, ta gauraya ta shafa akan fuskar, ta barshi zuwa kamar minti biyar sai ta wanke. Idan ya bushe ta shafa man zaitun.

In sha Allahu ƙurajen fuskar zasu mutu, kuma duk wani tabo ko baƙi-baƙi zai washe daga kan fuskarta.

Allah yasa mudace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button